Siyasar Najeriya
Mawakin Afrobeats Davido ya yi murnar sake zaben kawunsa Ademola Adeleke a matsayin gwamnan Osun, bayan hukumar zabe ta INEC ta tabbatar da nasarar.
An lakada wa ɗan jaridar TheCable duka a rumfar zaɓen ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji yayin zaɓen jihar Osun, kafin ’yan sanda su shiga tsakani su kare shi.
Atiku Abubakar ya taya Ademola Adeleke murnar sake lashe zaɓen gwamnan Osun, bayan INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara da ƙuri’u 511,067.
Gwamna Ademola Adeleke na Accord ya lashe kananan hukumomi 19 a zaben jihar Osun, yayin da Bola Oyebamiji na APC ya samu nasara a kananan hukumomi 11.
Jigon Accord, Pelumi Olajengbesi, ya ce Tinubu ya taya Adeleke murnar nasarar zaben Osun kafin sanar da sakamakon, yana yaba wa shugaban kasar kan rashin tsoma baki.
Kwamitin kamfen Gwamna Adeleke ya zargi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da shirya ayyana zaɓen gwamnan jihar Osun a matssyin wanda bai kammalu ba.
Sakamakon zaben gwamnan Osun na yau Asabar ya fara fitowa daga rumfunan zabe bayan kammala kada kuri'u, tuni dai malaman zabe na INEC suka fara kidaya kuri'u.
Mawaki Davido ya ce Ademola Adeleke na kan gaba a zaben Osun, ya kuma bukaci al’umma su kasance cikin taka-tsantsan yayin da ake tattara sakamakon zaben.
APC ta yi nasara a rumfar Kayode Adereti da tazarar ƙuri’u shida, yayin da ta doke Accord da gagarumar tazara a rumfar Rauf Aregbesola a jihar Osun.
Siyasar Najeriya
Samu kari