Wike: APC Ta Kifar da Mutanen Fubara wajen Tantance 'Yan Takarar 2027

Wike: APC Ta Kifar da Mutanen Fubara wajen Tantance 'Yan Takarar 2027

  • Magoya bayan gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara sun fuskanci matsala yayin da jam'iyyar APC ke tantance masu neman takara a zaben 2027
  • Rahoto ya nuna cewa kwamitin ya kifar da manyan na hannnun daman gwamna Fubara da suka halarci wajen tantance masu son tsayawa takara
  • A daya bangaren kuma, yawancin mutanen da ke biyayya ga ministan Abuja, Nyesom Wike da ya yi takun saka da Fubara sun tsallake tantancewar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Kwamitin tantance ’yan takara na jam’iyyar APC ya hana tsohon kakakin tsagin majalisar dokokin jihar Rivers, Victor Oko Jumbo takara.

Baya ga Jumbo, kwamitin ya hana wasu masu neman takara 64 shiga zaɓen fidda-gwani na majalisar dokokin jihar domin zaɓen 2027 mai zuwa.

Gwamna Siminalayi Fubara
Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara na bayani a wajen taro. Hoto: Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa yawancin ’yan takarar da aka hana shiga gasar manyan magoya bayan gwamnan jihar Rivers ne, Siminalayi Fubara.

Kara karanta wannan

SDP 2027: Jam'iyyar adawa ta farko ta tsaida ɗan takarar shugaban kasa

Dalilin hana mutane takara a Rivers

Rahoton kwamitin tantancewar da shugaban kwamitin, Muraina Ajibola da wasu mambobi uku suka sanya wa hannu, ya nuna cewa an hana ’yan takarar ne saboda sun gaza cika sharudan da ake buƙata.

Sai dai kwamitin ya amince da ’yan takara 33 masu biyayya ga ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike kuma yawancinsu mambobin majalisar dokokin jihar Rivers ne masu ci.

Kwamitin ya ce ya tantance takardun waɗanda aka amince da su cikin nasara kuma sun cika ƙa’idojin cancantar shiga zaɓen fidda-gwanin jam’iyyar.

Wasu da aka amince da su

Daga cikin waɗanda aka amince da su akwai Maol Dumle da Major M. Jack da Nwabochi Frankline da Ofiks K. Christopher da Enemi Alabo George da Tonye Smart Adoki da Tekenari W. Granville da Azeru Opara da Igwe Obey Aforji.

Opuende Lolo Isaiah da Ukalikpe Napoleon da Hope Ugwumadu da Kenneth Minimah da Justina Aniton Okorji da Onyema Rex Nwankwo da Jumbo Soparagha da Wami Solomon da Peter E. Abbey na cikinsu.

Kara karanta wannan

Fada ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a Zamfara, an kashe hatsabibin jagora

Sauran sun haɗa da Loolo Bulabari Henrietta da Barida Alice Samuel da Ohanuna Bright da Kue Yeghene Nwankwo Chimezie C. da Emeji Gloria Chika da Ejekwu da Ezebunwo Leslie da Okpokipou Peters da Arnold O. Davids.

Korafin magoya bayan Fubara

Daga cikin fitattun ’yan takarar da aka hana shiga har da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Obio/Akpor kuma babban masoyin Fubara, Chijioke Kemzunum Ihunwo da wasu.

Punch ta ce jimillar ’yan takara 98 ne suka sayi fom ɗin tsayawa takara domin shiga zaɓen fidda-gwanin APC na majalisar dokokin jihar Rivers, kuma sun halarci tantancewar da aka yi.

Nyesom Wike a wajen taro a Abuja
Ministan Abuja, Nyesom Wike na bayani a wajen taro. Hoto: Lere Olayinka.
Source: Twitter

Wani mai goyon bayan Fubara ya shaida cewa matakin jam’iyyar na iya bai wa kowace jam’iyyar adawa mai ƙarfi damar lashe jihar Rivers a zaɓen 2027.

Ya ce:

“Ba za ku kori manyan masu jan jama’a daga jam’iyya kawai saboda kuna son faranta wa wata ƙungiya rai ba, sannan ku yi tsammanin za su zauna su yi aiki domin nasarar mutanen da suka zalunce su.
“Duk da muna tafiyar da lamarin a matsayin jam’iyya, amma idan ba a kula da shi yadda ya kamata ba, ina ganin APC ta cutar da kanta, kuma za a ga sakamakon hakan a babban zaɓe.”

Kara karanta wannan

Kallo ya koma sama yayin da APC ta tantance gwamnoni 14 babu sunan Fubara

Gwamnan Imo zai yi takarar Sanata

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnan Imo ya sanar da cewa zai tsaya takarar sanata a babban zaben shekarar 2027.

Gwamna Hope Uzodimma zai tsaya takarar sanata ne duk da cewa sai a shekarar 2028 wa'adin shi na biyu na gwamna zai kare.

Hakan ya haifar da rade-radin cewa gwamnan zai yi murabus domin fatan samun kujerar shugaban majalisar dattawa idan ya ci zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng