Lamari Ya Baci: 'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Sace Dalibai da Dama a Borno

Lamari Ya Baci: 'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Sace Dalibai da Dama a Borno

  • 'Yan ta'addan Boko Haram dauke da makamai sun kai hari da sanyin safiya a wasu makarantu da ke jihar Borno ta tarayyar Najeriya
  • Tsagerun 'yan ta'addan sun kai farmakin ne bayan sun jira jami'an tsaron da ke aikin sintiri sun bar yankin
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ana fargabar 'yan ta'addan sun yi awon gaba da dalibai masu yawa zuwa cikin daji bayan kawo harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Ana fargabar 'yan ta'addan Boko Haram sun sace dalibai da ba a san adadinsu ba a jihar Borno.

'Yan ta'addan sun sace adadin ɗaliban da ba a tantance ba na makarantar firamare da karamar sakandare ta Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno.

'Yan Boko Haram sun kai hari a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa 'yan ta'addan na Boko Haram sun kai harin ne da sassafe a ranar Juma’a, 15 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Yadda harin sojojin sama ya hallaka farar hula da 'yan ta'adda a Zamfara

Mussa wani matsakaicin ƙauye ne mai nisa kuma yana iyaka da dajin Sambisa, wanda matakarar ’yan ta’adda ce da kuma maboyarsu.

Majiyoyi sun bayyana cewa ’yan ta'addan sun fado makarantar ne a kan babura, mintuna 10 ko 15 bayan da dakarun sojoji suka bar yankin.

A halin da ake ciki, mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Borno, Rt Hon. Abdullahi Askira, wanda shi ma ɗan Ƙaramar Hukumar Askira-Uba ne, ya tabbatar da harin da ’yan ta’addan suka kai makarantar ranar Juma’a.

Mataimakin shugaban majalisar dokokin ya ce har yanzu bayanai ba su kammala ba a daidai lokacin haɗa wannan rahoto.

“Haka ne, zan iya tabbatar muku cewa wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne a kan babura sun far wa makarantun firamare da ƙaramar sakandare a ƙauyen Mussa a safiyar yau."

“Bayanin da nake da shi shi ne, da yawa daga cikin ɗaliban sun gudu zuwa cikin daji, amma har yanzu ba ni da cikakken bayani kan waɗanda aka sace.”

“Abin baƙin ciki kuma shi ne, lamarin ya faru ne ’yan mintuna kaɗan bayan da dakarun sojoji masu sintiri suka bar yankin; wannan yana nuna cewa ’yan ta'addan ko maharan suna leƙen zirga-zirgar sojojin ne kafin su kawo harin."

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda, an kashe manyan kwamandojin Boko Haram a Borno

- Abdullahi Askira

Sai dai ya yi alƙawarin bayar da ƙarin bayani yayin da abubuwa ke ci gaba da bayyana.

Duk wani ƙoƙari na tuntuɓar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Borno, ASP Keneth Daso, domin ya yi tsokaci kan lamarin ya gaza haifar da ɗa mai ido a daidai lokacin haɗa wannan rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng