Sanata Kwankwaso Ya Fito da Bayanai game da Dalilansu nas barin ADC

Sanata Kwankwaso Ya Fito da Bayanai game da Dalilansu nas barin ADC

  • Tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce matsalolin da suka jawo ficewarsa daga ADC kusan iri daya ne da wanda ya jawo ya bar NNPP
  • Ya zargi matsalolin shari’a da siyasa kan rajistar ADC da aka yi ƙoƙarin soke wa a matsayin daya daga cikin rigigimun da suka sanya su sauya sheka
  • Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kara da bayyana cewa a yanzu, abin da suka saka a gaba shi ne hada kan 'yan Najeriya a kan zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa matsalolin da suka sa suka fice daga jam’iyyar NNPP sun yi kama da irin rikice-rikicen da suka fuskanta a lokacin da suke cikin haɗakar ADC.

Kara karanta wannan

Da sake: Amnesty ta nemi a bi jinin matasan Kano da aka kashe bayan naɗa Garo

Ya bayyana hakan ne kwanaki bayan sauya shekarsa daga haɗakar hamayyar ADC zuwa sabuwar tafiya ta NDC wadda ke ci gaba da jan hankali a siyasar Najeriya.

Sanata Kwankwaso ya ce rigingimu ne ya kore su daga ADC
Kwankwaso tare da manyan NDC a Abuja Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da DW, Kwankwaso ya bayyana dalilan da suka sa suka fice daga ADC da kuma yadda suke ganin makomar siyasar haɗaka a Najeriya.

Kwankwaso: "Dalilin da ya sa na bar ADC"

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce sun gano cewa an shiga wani yanayi da ake ƙoƙarin shafar rajistar jam’iyyar ADC ta hanyar shari’a, abin da ya ce ya zama barazana ga tafiyar siyasa mai gaskiya.

Ya ce:

"Yayin da muka shiga, musamman ita gwamnati ko mu ce APC, da suka ga yadda jama'a suka shigo APC, watakila irin ganin yadda muka hadu, suna ganin za ta zamar wa gwamanti barazana. Ana wannan sai muka samu labarin shi k ansa ministan shari'a da kansa ya tafi babbar kotu don ganin yadda za a soke rajistarmu."

Ya kara da cewa a yayin da ake cikin wannan rikici, an kuma samu wata kotu da ta yanke hukunci kan dakatar da dukkan tarukan jam’iyyar a matakin jihohi da na ƙasa baki ɗaya, lamarin da ya ce ya ƙara rikitar da yanayin siyasar cikin haɗakar.

Kara karanta wannan

Kano: Gawuna ya bi sahun Kwankwaso, ya bayyana dalilinsa na barin ADC

Babu rikici a NDC, cewar Kwankwaso

Kwankwaso ya bayyana cewa babu wani babban rikici ko sabani a cikin sabuwar jam’iyyar NDC da ya sa suka shiga cikinta, yana mai cewa abin da ake gani a baya ba ya wuce rashin fahimta ne kawai da aka riga aka warware.

Kwankwaso ya ce ana son hada kai don samun nasarar NDC
Alamar jam'iyyar NDC da ke tashe yanzu a Najeriya Hoto: National Democratic Congress, NDC Kano branch
Source: Facebook

A kan batun raba tikitin takarar shugaban ƙasa zuwa Kudancin Najeriya, ya ce batun yana cikin tattaunawa a tsakanin jam’iyyar, kuma za a fitar da matsaya nan gaba.

Ya ce a yanzu babban abin da ya fi muhimmanci shi ne haɗa kan ‘yan Najeriya tare da tabbatar da cewa dukkanin ɓangarori sun yi aiki tare domin samun nasara a zaɓen da ke tafe.

Kwankwaso ya magantu kan rajitsa a NDC

A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya bukaci magoya baya su gaggauta yin rajista da jam’iyyar NDC gabanin wa'adin hukumar zabe ta kasa INEC.

Ya yi kiran ne bayan shi da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi suka sanar da sauya sheka daga hadakar adawa ta ADC zuwa NDC karkashin Serieke Dickson saboda wasu dalilai.

Kara karanta wannan

NDC: Kwankwaso ya mika sakon kar ta kwana gabanin rufe rajistar jam'iyyu a Najeriya

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya jaddada muhimmancin yin rajista kafin karshen wa'adin, musamman ga wadanda ke da niyyar kawo canji a Najeriya gabanin babban zaben 2027 mai zuwa.s

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng