Bidiyo: Rikici Ya Barke tsakanin Gwamnonin APC a Taron Abuja, PGF Ta Dare Gida 2

Bidiyo: Rikici Ya Barke tsakanin Gwamnonin APC a Taron Abuja, PGF Ta Dare Gida 2

  • Wani babban rikicin shugabanci ya ɓalle a cikin ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC (PGF), inda gwamnonin suka dare zuwa gida biyu
  • Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya nace cewa har yanzu shi ne halastaccen shugaban PGF, kuma Uba Sani na Kaduna ne mataimakinsa
  • Wani ɓangaren gwamnonin kuma sun kafa tasu ƙungiyar a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dapo Abiodun Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Wani babban rikicin shugabanci ya barke a ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC (PGF), yayin da aka samu ɓallewar wasu mambobi, suka kafa nasu shuganancin.

Tun da fari, gwamnan Imo kuma shugaban ƙungiyar PGF, Hope Uzodimma, ya jaddada cewa shi ne har yanzu yake jagorancin PGF tare da mataimakinsa, Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna.

Rikici ya barke a kungiyar gwamnonin APC.
Gwamna Hope Uzodimma ya yi jawabi a taron tsaginsu na kungiyar gwamnonin APC. Hoto: @Hope_Uzodimma1
Source: Twitter

Kungiyar gwamnonin APC ta dare gida 2

To sai dai, rahoton da Arise News ta fitar ya nuna cewa wani babban ɓangare na gwamnonin ya janye goyon bayansa ga Hope Uzodimma, tare da zabar sababbin shugabanni.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi garambawul a majalisar zartarwa da kwamishinoni 2 suka ajiye aiki

Wannan tsagin ya nuna goyon baya ga Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, a matsayin shugabannin PGF ta ɓangaren su.

Wannan lamari ya nuna babban tsagewa a cikin gwamnonin na APC gabanin shiga zaɓukan shekarar 2027, sannan yana zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa a jam’iyya mai mulki.

Abin da ya jayo rikicin gwamnonin APC

Majiyoyi a cikin jam’iyyar sun bayyana cewa tashin hankali ya daɗe yana ruruwa a cikin ƙungiyar game da iko da shugabanci, da kuma yadda kowane ɓangare ke son sanya kansa a matsayin mai faɗa a ji gabanin kakar zaɓe mai zuwa.

Ana sa ran wannan baraka za ta janyo sababbin lissafin siyasa a cikin jam’iyyar APC, musamman ganin cewa gwamnoni ne manyan masu iko a cikin tsarin jam’iyyar na ƙasa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu ɓangaren da ya fitar da cikakkiyar sanarwa ta hukuma da ke bayyana asalin abin da ya janyo wannan rarrabuwar kai.

Gwamnonin da suka yi wa Uzodimma tawaye

Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa kusan gwamnoni 20 ne suka halarci wani taron sirri da aka gudanar, wanda ya haɗa da gwamnonin jihohin Ogun, Bayelsa, da kuma Enugu.

Kara karanta wannan

Abba ya yi tattaki zuwa Abuja, ya mika fam neman takarar gwamnan Kano

Wannan taron ya fito da irin rarrabuwar kawunan da ke tsakanin shugabannin jihohin game da ci gaba da kasancewar Gwamna Hope Uzodimma a matsayin shugaban ƙungiyar PGF.

An samu tsagin gwamnonin APC da suka ki amincewa da shugabancin Gwamna Hope Uzodimma.
Gwamna Uba Sani ya na jawabi a taron kungiyar gwamnonin APC tsagin Hope Uzodimma a Abuja. Hoto: @Hope_Uzodimma1
Source: Twitter

A cewar majiyoyin, gwamnonin da aka ce sun kaɗa ƙuri’ar rashin amincewa da Uzodimma sun fito ne daga jihohi 13 waɗanda suka haɗa da:

  • Adamawa
  • Zamfara
  • Delta
  • Akwa Ibom
  • Cross River
  • Rivers
  • Bayelsa
  • Niger.
  • Kwara
  • Plateau
  • Enugu
  • Ogun
  • Katsina

Duk da wannan tawaye, Uzodimma ya samu gagarumin goyon baya daga wasu gwamnonin na APC guda 16. Waɗannan gwamnonin sun haɗa da na jihohin: Yobe, Legas, Gombe, Kogi, Edo, Ekiti, Ondo, Sokoto, Jigawa, Taraba, Ebonyi, Benue, Kano, Kebbi, Nasarawa, da kuma Kaduna.

Kalli bidiyon taron tsagin Hope Uzodimma a kasa:

Shettima ya hadu da gwamnonin APC

A wani labari, mun ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya mika fom din neman tsayawa takara da Shugaba Bola Tinubu ya saya ga jam'iyyar APC.

A wani taro da aka yi a Abuja, wanda ya samu halartar gwamnonin APC, Shettima ya bukaci 'yan Najeriya su goyi bayan Bola Tinubu a zaben 2027 domin a cewarsa ya kawo cigaba.

Shugaba jam'iyyar APC na kasa ya halarci taron, inda ya bayyana cewa Bola Tinubu ya kawo cigaba sosai a shekara hudu da ya kusa cikawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com