ADC: Tsohon Minista, Amaechi Ya Zama na 2 da Ya Sayi Fam na Takarar Shugaban Kasa a 2027
- Rotimi Amaechi ya sayi fam din nuna sha'awa da shiga tseren neman takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar adawa ta ADC
- jigon ADC kuma shugaban kwamitin manufofi na jam’iyyar, Cif John Odigie-Oyegun, ne ya jagoranci tawagar da ta karbi fam a madadin Amaechi
- Tsohon ministan ya sha bayyana cewa yana da gogewar da idan ya samu damar hawa mulki, zai warware matsalolin da suka addabi kasar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya sayi fam ɗin nuna sha’awa da tsayawa takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar adawa ta ADC a shirye-shiryen tunkarar zaben 2027.
Babban jigon ADC kuma shugaban kwamitin manufofi da kundin tsarin jam’iyyar, Cif John Odigie-Oyegun, ne ya jagoranci wata tawaga zuwa sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja domin karɓar fom ɗin a madadin Amaechi.

Kara karanta wannan
Hayatudeen: Mai neman takarar shugaban kasa ya riga Atiku sayen fom din ADC, ya dauki alkawura

Source: Facebook
Amaechi ya sayi fam din takara a ADC
Sanata Abatemi-Usman na cikin tawagar da ta karɓi fom ɗin a ranar Juma’a, 8 ga watan Mayu, 2026, kamar yadda jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito.
Amaechi dai ya taba rike kujerar kakakin majalisar dokokin Ribas da kuma gwamnan jihar na tsawon wa'adi biyu, kafin daga bisani a nada shi Ministan Sufuri a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari.
Tsohon gwamnan ya shiga tseren neman takarar shugaban kasa ne bayan samun goyon baya daga sassa daban-daban, musamman shugabannin ADC daga yankin Kudu maso Kudu.
Mutum 2 sun karbi fam a ADC
Amaechi ya zama na biyu da ya sayi wannan fom na nuna sha'awar tsayawa takarar kujera lamba daya a jam'iyyar ADC, wanda kuɗinsa ya kai Naira miliyan 90.
Kafin shi, Alhaji Mohammed Hayatu-Deen ya riga ya sayi fom ɗin domin nuna aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin ADC a zaɓen 2027.
Amaechi ya sha bayyana cewa Najeriya na buƙatar shugabanci mai ƙwarewa tare da bai wa matasa dama da kuma ci gaba da tsarin karba-karba tsakanin yankunan kasar nan.

Source: Facebook
Amaechi ya shirya tunkarar matsaloli
Ya kuma ce tsaro, tattalin arziki da bunƙasa ababen more rayuwa su ne manyan abubuwan da ya kamata gwamnatin gaba ta mayar da hankali a kai domin gina gobe mak kyau ga yan Najeriya.
A cewarsa, gogewarsa a harkar mulki da ayyukan raya ƙasa sun isa shaidar da za ta nuna ya cancanci a ba shi dama a 2027 domin tinkarar matsalolin Najeriya, kamar yadda Vanguard ta kawo.
“Na san matsalolin ƙasar nan kuma ina da ƙwarewar da zan iya magance su,” in ji Amaechi.
Amaechi ya hango faduwar Tinubu a 2027
A wani labarin, kun ji cewa Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ’yan Najeriya da dama suna ɗokin ganin sun kori Shugaba Bola Tinubu daga kan mulki a zaɓen shekara mai zuwa.
Amaechi ya bayyana tabarbarewar yanayin tattalin arziƙi da ƙaruwar wahalhalu a faɗin ƙasar a matsayin dalilan da za su sa yan Najeriya su maida Shugaba Tinubu gida a 2027.
Tsohon ministan sufurin ya kuma soki yadda ake amfani da ƙabilanci da addini a siyasa, yana mai nuna cewa hakan ya taimaka wajen kawo yanayin da ake ciki yanzu.
Asali: Legit.ng
