Tsugune ba Ta Ƙare ba: Kotu Ta Ɗage Shari'ar Rikicin Shugabancin ADC a Abuja

Tsugune ba Ta Ƙare ba: Kotu Ta Ɗage Shari'ar Rikicin Shugabancin ADC a Abuja

  • Jam’iyyar ADC na fuskantar sabon rikicin shugabanci bayan kotun tarayya da ke Abuja ta dage shari’ar da aka shigar
  • Hon. Nafiu Bala Gombe ne ya shigar da kara inda yake neman a dakatar da shugabancinta bangaren David Mark
  • Lauyan mai kara ya bayyana cewa Kotun Koli ta yi watsi da karar daukaka kara da David Mark ya shigar, sannan ta soke dakatarwar shari’ar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kotun Tarayya da ke Abuja ta sake zama game da korafin shugaban tsagin ADC a Najeriya, Nafiu Bala Gombe.

Kotun ta dage shari’ar da Nafiu Bala ya shigar kan shugabancin jam’iyyar karkashin jagorancin David Mark.

Kotu ta dage shari'ar rikicin shugabancin ADC
Hagu zuwa dama: David Mark, Nafiu Bala Gombe da Atiku Abubakar. Hoto: @atiku, @SenDavidABMark, @Imranmuhdz.
Source: Twitter

Mai shari’a Emeka Nwite ya dage karar ba tare da sanya sabuwar rana ba bayan mai kara ya sanar da kotu cewa ya nemi a sauya alkalin da ke sauraron shari’ar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

An soki Ganduje kan kalamai mabambanta game da sahihancin sarautar Sanusi II

Matsayar kotun kan rikicin shugabancin ADC

Shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025 ta haifar da sabon rikici a cikin ADC bayan bayyanar David Mark da tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, a tsarin shugabancin jam’iyyar.

A zaman kotun, lauyan mai kara Luka Musa Haruna ya ce Kotun Koli ta yi watsi da karar daukaka kara da David Mark ya shigar saboda rashin cancanta.

Haruna ya kara da cewa Kotun Koli ta kuma soke umarnin Kotun Daukaka Kara da ya dakatar da ci gaba da sauraron shari’ar.

Sai dai ya bayyana cewa mai karar ya rubuta wasika zuwa ga babban alkalin kotun tarayya ranar 4 ga Mayu, 2026 domin neman a mayar da shari’ar hannun wani alkali daban.

An dage karar Nafiu Bala a kotun tarayya
Shugaban tsagin jam'iyyar ADC a Najeriya, Nafiu Bala Gombe. Hoto: Hon Nafiu Bala.
Source: Facebook

Lauyoyi sun yi muhawara mai zafi

Lauyoyin wadanda ake kara sun nuna adawa da bukatar, inda suka zargi mai karar da kokarin hana a ci gaba da sauraron shari’ar cikin gaggawa.

Lauyan wanda ake kara na farko, Realwan Okpanachi, ya ce ba su samu wani bayani kan bukatar sauya alkalin ba, yana mai bayyana matakin a matsayin bazata.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kungiyar Obidient ta canza suna, ta kori Peter Obi da Yunusa Tanko

Shi ma lauyan wanda ake kara na biyu, Sulaiman Usman, ya bayyana matakin a matsayin neman kotun da za ta fifita mai kara, cewar Daily Post.

Lauyan wanda ake kara na biyar, P.I. Oyewole, ya ce mai karar na kokarin jawo babban alkalin kotu cikin abin da ya kira rashin da’a a harkar shari’a.

A hukuncinsa, Mai shari’a Emeka Nwite ya ce kotun ba za ta iya daukar wani mataki kan wasikar ba tare da sauraron bangarorin biyu ba.

Ya ce yin hakan zai saba wa hakkokin wadanda ake kara, saboda haka kotun ta dage shari’ar ba tare da sanya rana ba domin jiran umarnin babban alkalin kotun tarayya.

Nafiu Bala ya musanta cewa yana cikin hatsari

A baya, an ji cewa shugaban tsagin ADC a Najeriya, Nafi’u Bala ya yi magana game da barazanar da aka ce an yi masa kan jam'iyyar adawa.

Nafiu Bala ya musanta rahoton da ke cewa ya yi nadamar rikicin jam’iyya tare da zargin rayuwarsa na cikin haɗari.

Ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya da farfaganda, yana mai cewa bai ba da wata hira ba kuma bai tura kowa ya yi magana madadinsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.