"Da Hannun Tinubu": ADC Ta Yi Fallasa kan 'Dalilin' Farfardo da Jam'iyyar NDC
- Sakataren yada labaran jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƙoƙarin raba kan adawa ta hanyar ƙirƙirar NDC
- Ya bayyana haka ne bayan jiga-jigan jam'iyyar da suka hadu don fatattakar gwamnatin APC sun fice tare da sauya sheka zuwa NDC gabanin 2027
- Bolaji Abdullahi ya ce gwamnatin Tinubu ta jefa mutane cikin talauci da wahala sakamakon manufofin tattalin arziƙinta da suka ci karo da rayuwar talaka
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam'iyyar ADC yi kakkausar suka ga yadda ake tafiyar da Najeriya inda ta zargi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da jawo manufofin da ke wahalar da talaka.
Sakataren yada labaran jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa abin da ake gani tsakanin bangaren zartarwa da majalisa zai iya rusa dimokuraɗiyya ba.

Source: Facebook
A hira da Bolaji Abdullahi ya yi da jaridar The Sun, ya soki gwamnatin APC, tare da zargin cewa da hannun Bola Ahmed Tinubu a cikin farfado da jam'iyyar NDC a Najeriya.
ADC na ganin Bola Tinubu ya gaza
BBC ta wallafa cewa Bolaji Abdullahi ya yi zargin tsoro ya gama dabaibaye shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya sha shi nema wa kansa mafta.
Da yake magana kan mulkin Tinubu, Bolaji Abdullahi ya ce bai ce shugaban ya gaza gaba ɗaya ba, amma ya kasa tuna wani fanni da zai ce gwamnatin ta yi abin a yaba.
Ya ce:
“Yana da wahala na tuna wani bangare da zan ce shugaban ƙasa ya yi abin kirki. Bangaren lafiya? Rayuwar jama’a? Mutane masu mutunci sun koma mabarata a ƙarƙashin wannan gwamnati saboda manufofinta marasa kyau.”
Ya kuma soki yawan kashe kuɗin gwamnati wajen tafiye-tafiye, yana mai cewa an kashe biliyoyin Naira yayin da ake roƙon talakawa su ƙara haƙuri.

Source: Twitter
Bolaji Abdullahi ya ce rahoton da ya nuna Tinubu na da 32% na karɓuwa daga jama’a ya nuna shugaban ƙasar zai iya shan kasa a zaben 2027.
Ya ce:
“Shugaban ƙasa mai 32% na karɓuwa a wurin jama'a shugaban ƙasa ne da za a iya kayarwa. Shi ya sa yake tsoro.”
Zargin da ADC ke yi wa Shugaba Tinubu
Jam'iyyar hadakar adawa ta ADC ta kuma zargin Tinubu da ƙoƙarin tayar da rikici a cikin ADC domin raunana adawar da za ta kalubalance shi a zabe mai zuwa.
A cewarsa:
“Shi ya sa suke yin duk abin da za su yi domin tarwatsa ADC, har da ƙirƙirar NDC domin raba kan adawa.”
Ya ƙara da cewa duk wanda ba ya goyon bayan haɗakar adawa domin fuskantar gwamnati, to yana aiki ne domin amfanin shugaban ƙasa.
Shettima, APC sun goyi bayan Tinubu
A baya mun kawo labarin cewa Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya mika fam din neman tsayawa takara da Shugaba Bola Tinubu ya saya ga jam'iyyar APC na zaben 2027.
A wani taro da aka yi a Abuja, Shettima ya bukaci 'yan Najeriya su goyi bayan Bola Tinubu a zaben 2027 domin a cewarsa ya kawo cigaba tare da dora wa daga inda zai tsaya a mulkinsa.
Shugaba jam'iyyar APC na kasa Farfesa Nentawe Yilwatda ya halarci taron, inda ya bayyana cewa Bola Tinubu ya kawo cigaba sosai a shekara hudu da ya kusa cikawa a mulkin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


