Jonathan Ya Kalubalanci Wanda Ya Nemi Hana Shi Fitowa Takarar Shugaban Kasa a 2027
- Goodluck Jonathan ya kalubalanci karar da aka shigar gaban babbar kotun tarayya da nufin hana shi fitowa takarar shugaban kasa a 2027
- Tsohon shugaban kasar ya nuna takaicinsa kan yadda aka shigar da karar duk da an taba yanke hukunci kan makamancin wannan batu
- Lauyansa, Cif Chris Uche (SAN), ne ya bayyana hakan a gaban Mai shari’a Peter Lifu na babbar kotun tarayya da ke Abuja
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya kalubalanci wata ƙara da wani lauya mai suna Johnmary Jideobi ya shigar domin hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.
Lauyan Jonathan, Cif Chris Uche (SAN), ne ya bayyana hakan a gaban Mai shari’a Peter Lifu na babbar kotun tarayya da ke Abuja bayan da aka kira shari’ar domin sauraro.

Source: Getty Images
Jonathan ya bukaci kotu ta kori karar
A rahoton da Daily Trust ta wallafa, Uche ya shaida wa kotun cewa sun riga sun shigar da takardar da ta bukaci kotun ta yi fatali da wannan kara tare da hujjjoji tun ranar 5 ga watan Mayu, 2026.
Ya ce sun samu labarin ƙarar ne ta kafafen yaɗa labarai, lamarin da ya sa suka gaggauta shigar da takardunsu saboda muhimmancin batun wanda ya shafi cancantar tsohon shugaban ƙasar wajen tsayawa takara a zaɓe mai zuwa.
Babban lauyan ya bayyana takaicinsa kan yadda wani lauya ya shigar da irin wannan ƙara duk da cewa an taɓa yanke hukunci kan makamancin batun daga babbar kotun tarayya har zuwa kotun ɗaukaka ƙara.
A nasa bangaren lauyan mai ƙara, Ndubuisi Ukpai, ya ce yana buƙatar ƙarin lokaci domin mayar da martani kan bayanan da tsohon shugaban kasar ya gabatar a gaban kotu.
Kotu ta dage zaman shari'ar Jonathan
Daga nan ne Mai shari’a Lifu ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 11 ga watan Mayu, 2026 da ƙarfe 2:00 na rana domin sauraron ƙin amincewar Jonathan da kuma ainihin ƙarar.
Kotun ta kuma bayar da umarnin aika sammaci ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da kuma Antoni Janar na Tarayya (AGF), waɗanda su ne na biyu da na uku a cikin waɗanda ake ƙara.
Abin da aka nemi kotu ta hana Jonathan
An ruwaito cewa lauyan, Johnmary Jideobi, ya buƙaci kotun ta haramta wa Jonathan tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 bisa hujjojin kundin tsarin mulki.
Ya roƙi kotun da ta bayar da umarnin da zai hana Jonathan gabatar da kansa ga kowace jam’iyyar siyasa domin neman takarar shugaban ƙasa.
Haka kuma ya buƙaci a hana INEC karɓar sunan Jonathan daga kowace jam’iyya ko wallafa shi a matsayin ɗan takara a zaɓe, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Source: Facebook
An shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/2102/2025 tun ranar 6 ga Oktoba, 2025, inda aka sanya Jonathan a matsayin wanda ake ƙara na farko, sai INEC da AGF a matsayin na biyu da na uku.
Jonathan ya yi maganar fitowa takara
A wani labarin, kun ji cewa wasu matasa sun ziyarci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan domin neman ya tsaya takara a babban zaben 2027.
Jonathan ya ce ya fahimci bukatun da matasan suka gabatar masa, amma bai bayyana aniyarsa ta shiga takarar shugaban kasa ba.
Ya ce zai tuntubi mutane da dama tare da yin nazari sosai kafin daukar matakin da ya dace kan tsayawa takara a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng


