"Ba Dai a Matsayin Rauni ba," Gwamna Radda Ya Kafa Sharadin Sulhu da 'Yan Bindiga

"Ba Dai a Matsayin Rauni ba," Gwamna Radda Ya Kafa Sharadin Sulhu da 'Yan Bindiga

  • Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba zs ta yi sulhu da yan bindiga a matsayin rauni ko gazawa ba
  • Malam Dikko Radda ya ce al'umma daga yankuna daban-daban sun zauna da yan bindiga kuma sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya
  • Ya ce matsalar tsaron da Katsina ke fuskanta na bukatar hadin gwiwar al'ummar domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sake jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta shiga tattaunawa da ‘yan bindiga saboda ta gaza ba.

Gwamna Radda ya ce aikin hadin gwiwar al’umma tare da kokarin jami’an tsaro shi ne kashin bayan dawo da zaman lafiya a fadin jihar.

Katsina.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda yana magana da mahalarta kwas na 48 daga kwalejin horar da sojoji ta Najeriya lokacin da suka kai masa ziyara Hoto: Office of the CPS, Katsina State
Source: Facebook

Leadership ta ce Radda ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin mahalarta kwas din manyan jami'ai na 48 daga Kwalejin Horo ta Rundunar Sojin Najeriya, a wata ziyarar da suka kai Katsina.

Kara karanta wannan

Bayan sun yi barazana, gwamnatin tarayya ta amince da karin alawus na 40% ga ma’aikata

Gwamna Radda ya nanata matsayarsa

Ya ce duk da cewa wasu al’ummomi a yankunan da matsalar tsaro ta shafa sun shiga tattaunawa da ‘yan bindiga tare da yin yarjejeniyoyin zaman lafiya, gwamnati tana nan daram kan bakarta na tabbatar da tsaro.

“Mun bayyana karara cewa gwamnati ba za ta tattauna da su a matsayi ita ce mai rauni ba, amma al’umma sun shiga tattaunawa cikin hikima, kuma a wasu lokuta hakan ya samar da sakamako mai kyau,” in ji shi.

Gwamna Radda ya ce matsalar rashin tsaro a Katsina ta fi nasaba da ayyukan ta’addanci irin su satar shanu da garkuwa da mutane, ba wai ta fuskar akida ba.

Saboda haka gwamnan ke ganin cewa shigar al’umma cikin lamarin yana da muhimmanci wajen magance matsalar gaba daya.

Tsarin da gwamnatin Katsina ta dauka

A cewarsa, gwamnatin ta rungumi tsarin tsaro na hadin gwiwar al’umma bayan ta fahimci cewa dakarun sojoji, ‘yan sanda da jami’an NSCDC kadai ba za su iya tsare dukkan yankunan da ke cikin hadari ba.

Kara karanta wannan

An saki sunayen kananan hukumomi 3 da Boko Haram ta tilasta wa biyan haraji a Yobe

“Mun fahimci cewa yawan jami’an soji, ‘yan sanda da NSCDC bai kai yadda ake bukata ba domin samar da tsaro yadda ya kamata a kasar nan. Shi ya sa muka rungumi tsarin tsaro na hadin gwiwar al’umma,” in ji gwamnan.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kafa rundunar Katsina Community Watch Corps, inda aka dauki matasa aka horas da su ta hannun jami’an tsaro domin taimakawa wajen tattara bayanan sirri da kuma kai dauki cikin gaggawa.

Gwamna Dikko.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda a wurin taro Hoto: ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Twitter

Dikko Radda ya ce tsaro ya fara dawowa

Gwamnan ya kara da cewa wannan shiri ya taimaka wajen inganta tsaro a yankuna da dama da a baya ba a iya shiga cikinsu, tare da dawo da ayyukan noma a wasu kananan hukumomi.

Radda ya kuma yabawa rundunar soji da sauran jami’an tsaro bisa sadaukarwar da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Katsina ta gano 'yan leken asiri

A baya, kun ji cewa Gwamna Radda ya bayyana cewa akwai "yan leƙen asiri" a cikin gwamnati, hukumomin tsaro, da kuma cikin al'ummomi waɗanda ke bai wa ' yan bindiga bayanai.

Radda ya bayyana cewa yaƙi da rashin tsaro na fuskantar cikas sakamakon wasu mutane da ke fallasa muhimman bayanan tsaro ga 'yan bindiga.

Ya nuna damuwa kan wannan lamari, yana mai cewa hakan ke dakile duk wani yunkuri da gwamnati ke yi domin dawo da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262