"Mu Kece Raini": Gwamnan Gombe Ya Yi Martani bayan Kafiyar Pantami da Goje
- Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya bayyan cewa kowane dan siyasa ya san iya karfinsa, saboda haka za a yi zaben fitar da gwani
- Ya bayyana haka ne bayan tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya ki amincewa da sulhu a APC
- Fitaccen malamin wanda ya nuna sha'awar tsaya wa takarar gwamna ya ce ba zai amince da abin da ya kira zalunci a neman mulki ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Gombe – Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya mayar da martani ga masu neman takarar jagorancin jihar a zaben 2027.
Wadansu daga cikin masuneman kujerar gwamna sun sun zarge shi da amfani da tasirinsa wajen zaɓen ‘yan takarar jam’iyyar APC domin zaɓen 2027 ba tare da cikakken tuntuba ba.

Source: Facebook
BBC ta ruwaito cewa cewa gwamnan ya bayyana cewa tsarin da aka bi yana daga cikin hanyoyin da jam’iyya da hukumar zaɓe suka tanada, yana mai cewa har yanzu ba a kammala tsarin ba.
Gwamnan Gombe ya yi nune
A ruwayar jaridar Leadership, sanatan da ke wakiltar Gombe ta Tsakiya, Mohammed Danjuma Goje, wanda ke neman sake komawa majalisar dattawa, ya ƙi amincewa da tsarin maslaha.
Haka kuma tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya nuna rashin gamsuwa da tsarin, inda ya jaddada bukatar bin doka da ƙa’ida wajen gudanar da zaɓen.
Farfesa Pantami ya kuma nuna cewa akwai yiwuwar amfani da hanyoyin shari’a domin neman adalci idan bukatar hakan ta taso.
Da yake magana a wata hira da manema labarai, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce tsarin da aka bi ya samu amincewar masu neman takara tun farko.
“Kowa ya san ƙarfinsa” - Gwamnan Gombe

Kara karanta wannan
"Haka Allah ya tsara," 'Dan takarar APC, Jamilu Gwamna ya nemi hadin kan Pantami a Gombe
Gwamnan ya bayyana cewa akwai hanyoyi uku da jam’iyya ke amfani da su wajen zaɓen ‘yan takara, waɗanda suka haɗa da zaɓen kai tsaye, zaɓen wakilai da kuma tsarin maslaha da suka zaɓa a wannan karo.
A cewarsa, tsarin maslaha shi ne mafi sauƙi kuma mafi dacewa wajen cimma matsaya cikin jam’iyya ba tare da rikici ba.

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa har yanzu akwai damar da masu neman takara za su iya shiga fafatawa domin neman mukaman siyasa daban-daban kafin a kai ga matakin ƙarshe.
Gwamna Yahaya ya kuma bayyana cewa kowane ɗan siyasa ya san irin ƙarfinsa da tasirin da yake da shi a tafiyar siyasar jihar.
A kalamansa: “Kowa ya san mataki ko darajarsa a harkar nan. Za a yi zaben fitar da gwani na gama gari tun da shi ake so a yi sai mu hadu mu kece raini."
Gombe: Pantami ya yi fatali da maslaha
A baya, mun kawo labarin cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya fito ya yi magana kan fitar da dan takara da gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta a jihar Gombe.
A wani zama da masu ruwa da tsaki na APC a gidan gwamnatin jihar Gombe, an sanar da Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin dan takara wanda jam'iyya ta ke ganin zai kai labari.
A martanin da ya yi kan lamarin, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya nuna cewa ba a bi ka'ida ba wajen fitar da dan takarar kuma zai kalubalanci abin da ya kira zalunci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
