Kwankwaso Ya San Makomarsa da NDC Ta Yi Matsaya kan Tikitin Takara
- Jam’iyyar NDC ta gudanar da muhimmin taro a Abuja inda ta fitar da matsaya game da tikitin takarar shugaban kasa a shekarar 2027
- NDC ta ware tikitin takarar shugaban kasa na zaben 2027 ga yankin Kudu, yayin da yankin arewa zai samu damar takara a 2031
- Jam’iyyar ta bayyana cewa za ta gudanar da zaben fitar da gwani maimakon tsarin maslaha, yayin da batun rabon tikiti ya kara zafafa a 2027
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar NDC mai adawa a Najeriya ta sanar da ware tikitin takarar shugaban kasa na zaben 2027 da ake tunkara.
Jam'iyyar NDC ta mika tikitin takarar shugaban kasa a 2027 ga yankin Kudu wanda za su rike na tsawon wa'adi daya zuwa shekarar 2031.

Source: Twitter
An cimma matsayar ne a yayin babban taron kasa na jam’iyyar da aka gudanar ranar Asabar, bayan kudurin da Afam Victor ya gabatar tare da goyon bayan Seyi Sowumi, cewar TheCable.
Yaushe yankin Arewa zai samu dama a NDC?
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa yankin Arewa ne zai samu damar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashinta a zaben shekarar 2031.
Rahotanni sun nuna cewa taron ya kuma tabbatar da dukkan mambobin kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar bayan kudurin da Sanata Victor Umeh mai wakiltar Anambra ta Tsakiya ya gabatar.

Source: Twitter
Shugabannin jam’iyyar sun ce tsarin rabon tikitin ya dace da manufofin NDC na tabbatar da daidaito da karba-karba tsakanin yankunan arewa da kudu.
Tikitin takara: Abin da Buba Galadima ya ce
Tun da fari, jigon siyasa kuma na hannun daman Rabiu Musa Kwankwaso, Buba Galadima ya bayyana cewa jam’iyyar ta riga ta yanke shawarar bai wa kudu tikitin shugaban kasa.
"Mun tura tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudu, babu wata matsala na rasa kuri'u, mun tura shi can."
Ya kuma bayyana cewa NDC za ta gudanar da zaben fidda gwani domin tantance dan takararta, sabanin tsarin maslaha da wasu jam’iyyu ke amfani da shi.

Kara karanta wannan
Hayatudeen: Mai neman takarar shugaban kasa ya riga Atiku sayen fom din ADC, ya dauki alkawura
Matakin ya zo ne yayin da ake ci gaba da sauya sheka da kulla sababbin kawance a siyasar adawa gabanin babban zaben 2027 da ake tunkara nan da watanni kadan.
Rahotanni sun nuna cewa rabon tikitin ya yi daidai da matsayar Peter Obi na goyon bayan karba-karba da daidaito tsakanin yankunan Najeriya a harkar shugabanci.
NDC ta warware rikicin cikin gida a Kano
A wani labarin, an ji cewa jam'iyyar NDC ta warware rikicin shugabanci a Kano, bayan wasu kalamai da shugaban jam'iyyar Hon. Husaini Isah Mai Riga ya fara jawo rikici.
Hon Mai Riga ya fito kafafen yada labarai yana zargin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya shigo NDC da mutanensa kuma za a tura su gefe.
Shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa ba za su taba lamunta ba a yi masu abin da ya kira ture kaza kwashe kwai gabanin zaben 2027 ba da ake tunkara a kasar.
Asali: Legit.ng
