Taraba: An Zargi Jami'an Tsaro da Cafke Shugaban Miyetti Allah da ke Neman Takarar Sanata
- Jami’an tsaro sun kama shugaban Miyetti Allah Kautal Horé, Bello Bodejo, a Jalingo da ke jihar Jalingo bayan ganawa da magoya baya
- Bodejo wanda ke neman kujerar Sanatar Taraba ta Tsakiya ta bayyana cewa ba zai janye daga takarar Sanatan da ya ke nema ba a karkashin APC ba
- Hadiminsa ya ce har yanzu ba su san inda aka tsare shi ko dalilin kama shi ba,kuma har yanzu babu wanda ya yi masu bayanin komai game da batun
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Taraba, Jalingo An kama shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Horé kuma mai neman takarar Sanatan Taraba ta Tsakiya a jam’iyyar APC, Bello Bodejo, a daddare a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu a birnin Jalingo.
Rahotanni sun nuna cewa Bodejo ya isa Jalingo ne da wani jirgin sama mai zaman kansa ta filin jirgin saman Danbaba Suntai Airport da misalin ƙarfe 1.20 na rana.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa dubunnan magoya bayansa daga ƙananan hukumomi biyar na yankin Sanatan Taraba ta Tsakiya ne suka tarbe shi bayan isowarsa babban birnin jihar.
Jami'an tsaro sun cafke Bodejo
Rahoton ya bayyana cewa mai taimaka wa Bodoje na masa na musamman, Umar, ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho cewa an kama ubangidansa ne bayan ya kai ziyara wasu ofisoshin jami’an tsaro tare da na kusa da shi.
A cewarsa, lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan Bodejo ya yi jawabi ga magoya bayansa a sakatariyar jam’iyyar APC ta jihar da ke Jalingo.
Umar ya bayyana cewa jami’an tsaron sun umarci waɗanda suka raka shi da su fita nan take, yayin da suka tsare Bodejo.
Ya ce:
“A yanzu haka ba mu san inda aka kai shi ba.”
An gano jami'an da suka kama Bodejo
Umar ya kara da cewa jami'an tsaron da suka taho tare da Bodejo daga babban birnin tarayya Abuja, su ne suka kama a Jalingo.

Source: Original
Ya ƙara da cewa:
“Jami’an tsaron da suka raka shi kuma suka ba shi kariya tun daga Abuja zuwa Jalingo su ne daga baya suka kama shi.”
“Har yanzu ba a sanar da mu dalilin kama shi ba, kuma babban abin da ke damunmu shi ne ba mu san inda ake tsare da shi ba."
Kafin kama shi, Bodejo ya bayyana wa manema labarai a sakatariyar APC cewa ya sayi fam ɗin takarar Sanata ne domin fafatawa a zaɓe, kuma ba zai janye wa kowane ɗan takara ba.
Ya kuma bayyana cewa kwamitin sasanci da aka ce gwamnan jihar, Agbu Kefas, ya kafa domin tattaunawa da masu neman takara a yankunan sanatoci uku na jihar bai taɓa tuntuɓarsa ba.
A cewarsa:
“Kwamitin sasancin da gwamna ya kafa bai tuntube ni ba, kuma ina mai bayyana cewa ba zan janye wa kowa ba duk da irin matsin lambar da za a yi.”

Kara karanta wannan
Bayan abin da ya faru, an haramta wa masu digirin girmamawa amfani da 'Dr' a Najeriya
Kungiyar Miyetti Allah ta nemi alfarma
A baya, mun wallafa cewa kungiyar Miyetti Allah ta yi martan ga Shugaban kasar Amurka, Donald Trump kan alakanta su da ta'addanci a Najeriya bayan an sako ta a gaba game da batun kisan kiristoci a Najeriya.
Kungiyar ta ce ana yi mata mummunar fahimta, tana nan a matsayin ƙungiyar kiwo mai zaman lafiya da ke fuskantar hare-hare daga wasu sassa daban daban, ba wai ita ce ke neman rayukan jama'a.
MACBAN ta bayyana cewa dubunnan makiyaya sun mutu ko an raba su da muhallansu, tana kuma neman Amurka ta tallafa wajen samar da mafita ba dora masu laifin kisan kiristoci ba.s
Asali: Legit.ng

