Takarar 2027: 'Yan APC Sun Barke da Zanga Zanga, an Yi Fashe Fashe a Oyo

Takarar 2027: 'Yan APC Sun Barke da Zanga Zanga, an Yi Fashe Fashe a Oyo

  • An samu tashin-hankali a ranar Alhamis a sakatariyar jam’iyyar APC ta jihar Oyo da ke Ibadan yayin da wasu mambobin jam’iyyar suka gudanar da zanga-zanga
  • Masu zanga-zangar, waɗanda suka taru a sakatariyar APC ta jihar, sun zargi shugabannin jam’iyyar da tauye dimokuraɗiyya ta hanyar kakaba ‘yan takara
  • Rahoto ya nuna cewa sun yi zargin cewa an yin watsi da muradun mambobin jam’iyyar domin fifita wasu manyan masu faɗa-a-ji a wajen fitar da 'yan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Wasu mambobin jam’iyyar APC a jihar Oyo da ke Kudancin Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a ranar Alhamis kan zargin kakaba ‘yan takara gabanin babban zaɓen 2027.

An bayyana cewa masu zanga-zangar sun mamaye sakatariyar jam’iyyar APC da ke Oke-Ado a ƙaramar hukumar Ibadan ta Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin gwamna ya samu tikitin takara, zai kara da Gwamnan Sokoto

Wajen zanga zangar APC a Oyo
Masu zanga-zanga a hedkwatar APC a Oyo. Hoto: Inside Oyo
Source: Facebook

Gargadin da 'yan jam'iyyar APC suka yi

Tun da farko, Punch ta wallafa cewa yayin taron shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da masu neman takara, 'yan APC sun gargaɗi jagorori kan amfani da kuɗi wajen zaɓen ‘yan takara.

Sun kara da cewa maimakon kakaba ‘yan takara ga mambobi, ya kamata shugabannin jam’iyyar su yi adalci ga duk masu neman takara ta hanyar gudanar da zaɓukan fidda gwani na gaskiya da adalci.

Tribune ta wallafa cewa masu zanga-zangar sun ce irin waɗannan matakai sun taɓa yin illa ga jam’iyyar a baya, suna ambaton babban zaɓen 2023 da ya wuce a matsayin misali.

An yi barna wajen zanga-zangar APC

Da yake tabbatar da faruwar zanga-zangar a Ibadan, babban birnin jihar, sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC, Olawale Sadare, ya ce:

“An ɗauki nauyin masu zanga-zangar ne domin kawo cikas ga zaman lafiyar da jam’iyyar ke da shi a yanzu.

Kara karanta wannan

2027: Masu neman takara sun cika sakatariyar APC da gidan shugaban jam'iyya

“’Yan daba ɗin da aka ce sun kai hari kan mambobin kwamitin gudanarwa na jihar, ma’aikata da sauran waɗanda suke a sakatariyar, sun zo ne dauke da makamai da laya, kuma sun zo da yawa domin aiwatar da mugayen ayyukansu.
“Hare-haren, waɗanda suka ɗauki kusan awa biyu, sun haifar da lalacewar motoci da ginin sakatariyar, inda gilasan mota, tayoyi, tagogin ofisoshi, ƙofofi da sauran kayayyaki suka lalace.
Shugaban jam'iyyar APC, Nentawe Yilwatda
Nentawe Yilwatda na yi wa 'yan APC jawabi a Abuja. Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

Ya kara da cewa:

“Lamarin hari ne da aka shirya...amma muna godiya da cewa babu wanda ya rasa ransa a hare-haren."

'Yan jam'iyyar APC sun taru a Abuja

A wani labarin, kun ji cewa masu neman takara a matakai daban-daban da magoya bayan su sun taru a hedikwatar APC da ake birnin tarayya Abuja.

Bayan kai wa karfe 4:00 na yamma APC bata fitar da sakamakon tantance masu neman takara ba, mutanen sun wuce gidan shugaban jam'iyyar na kasa.

'Yan siyasar sun taru ne domin sanin ko sun tsallake matakin tantance 'yan takara da suka saye fom domin zuwa matakin zaben fitar da gwani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng