An Fara Tara Kudin Saya wa El Rufai Fam din Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027

An Fara Tara Kudin Saya wa El Rufai Fam din Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027

  • An bude asusun fara tara kudin saya wa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir E-Rufai fam din neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC
  • Kungiyar magoya bayan El-Rufai ta ESG ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa, duk da jigon na ADC na tsare a hannun hukumomin Najeriya
  • Masana na ganin wannan yunkuri da magoya baya suka fara na nuna alamun cewa da yiwuwar El-Rufai ya shiga neman takarar shugaban kasa a 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, sun kaddamar da asusun tara kuɗi daga jama’a domin sayen fam ɗin takarar shugaban kasa na 2027.

Magoya bayan sun fara yunkurin tara Naira miliyan 90 domin saya wa Malam Nasir El-Rufai fam din nuna'a sha'awa da tsayawa takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC duk da cewa har yanzu yana tsare a hannun Hukumar ICPC.

Kara karanta wannan

2027: Mata 6 da suka nuna sha'awar takarar gwamna a Najeriya

Nasir El-Rufai.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a taron jam'iyyar hadaka, ADC Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Ƙungiyar El-Rufai Support Group (ESG) ce ta sanar da hakan, lamarin da ya ƙara jawo muhawara a fagen siyasar Najeriya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta bayyana cewa ta yanke shawarar jagorantar sayen fam ɗin neman takara da nuna sha’awa na jam’iyyar ADC a madadin El-Rufai.

Dalilin fara tara masa kuɗin fam

Ƙungiyar ta ce matakin ya biyo bayan matsin lamba daga magoya baya da abokan siyasar Nasir El-Rufai da ke bukatar ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027.

A cewar sanarwar, tara kuɗin ba wai dole ba ne amma an fara yunkurin ne domin bai wa magoya baya daga sassan ƙasar nan damar bayar da gudunmawa wajen sayen fam ɗin.

Ƙungiyar ESG ta kuma yi ikirarin cewa cikin awa huɗu kacal da fara wannan shiri, an tara sama da Naira miliyan 45.75, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

El-Rufai na tsare a hannun ICPC

Kara karanta wannan

APC ta tara N4.4bn daga sayar da fam na takarar 2027 duk da rikicin jam'iyya

Wannan mataki na zuwa ne yayin da El-rufai ke ci gaba da zama a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC kan zargin almundahana a lokacin mulkinsa na Kaduna.

Ci gaba da tsare shi ya haifar da mabambantan ra’ayoyi a siyasa, inda magoya bayansa ke zargin ana yi masa bita da kullin siyasa, yayin da ICPC ke cewa tana bin doka wajen gudanar da bincike.

ADC .
Tutar jam'iyyar dakar yan adawar Najeriya, watau ADC Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

Ana ganin alamar shirin takarar El-Rufai

Masu sharhi kan siyasa na ganin fara tara kuɗi duk da cewa El-Rufai na tsare wata alama ce da ke nuna ƙoƙarin ci gaba da gina masa karfin siyasa gabanin zaɓen 2027.

El-Rufai, wanda ya taba zama ministan Abuja kuma gwamnan Kaduna na wa’adi biyu, na daga cikin fitattun ’yan siyasar Arewa masu tasiri da kuma jawo ce-ce-ku-ce.

Sai dai ko a watan Afrilu, El-Rufai ta bakin Muyiwa Adekeye ya karyata zancen cewa yana da burin neman takarar shugaban kasa a zaɓen shekara mai zuwa.

'Dan El-Rufai ya bar APC zuwa ADC

A baya, kun ji cewa Bello El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa ADC.

Kara karanta wannan

Yaron Atiku Abubakar ya sayi fam a ADC, zai nemi takarar sanata a Adamawa

Kakakin Majalisar Wakilai , Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ne ya karanta wasiƙar sauya shekar Bello El-Rufai a zaman majalisar na ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu, 2027.

Bello El-Rufai ya tabbatar da cewa zai sake neman takarar kujerar Majalisar wakilai a mazabar Kaduna ta Arewa karkashin inuwar jam'iyyar ADC a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262