2027: Nafiu Bala Ya Sake Birkita ADC bayan Fara Sayar da Fom din Takara

2027: Nafiu Bala Ya Sake Birkita ADC bayan Fara Sayar da Fom din Takara

  • Tsagin jam'iyyar ADC da Nafiu Bala ke jagoranta ya gargadi bangaren David Mark da ya dakatar da sayar da fom din neman takarar da ya fara
  • Ya yi gargadin ne bayan Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen sun riga sun saye fom domin neman shiga takara a 2027
  • Sakataren kwamitin amintattu na ADC bangaren Nafiu Bala, Rufus Akanmi ya yi magana kan hukuncin da kotun koli ta yi game da jam'iyyar a baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsagin ADC ƙarƙashin jagorancin Nafiu Bala ya buƙaci bangaren da David Mark ke jagoranta da ya dakatar da sayar da fom ɗin neman tsayawa takara har sai an kammala shari’ar da ke gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan

ADC: Tsohon minista, Amaechi ya zama na 2 da ya sayi fam na takarar shugaban kasa a 2027

Lamarin na zuwa ne yayin da babbar kotun tarayya ta ɗage shari’ar shugabancin jam’iyyar da Nafiu Bala ya shigar ba tare da sanya wata sabuwar rana ba.

Nafiu Bala da ke shugabantar tsagin ADC
Nafiu Bala a wajen wani taron ADC. Hoto: Hon. Nafiu Bala
Source: Facebook

Punch ta wallafi cewa sakataren kwamitin amintattu na ADC, Rufus Akanmi ne ya fitar da sanarwar gargadin a Abuja ranar Juma’a, 8 ga Mayu, 2026.

Tsagin Nafiu Bala ya gargadi ADC

Tsagin Nafiu Bala ya ce buƙatar dakatar da sayar da fom ɗin na cikin matsayar da aka cimma a taron kwamitin amintattun jam’iyyar da aka gudanar ranar Alhamis.

Ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya ci gaba da sayen fom ɗin takara bayan wannan umarni da ya bayar to ya yi kuka a kan shi.

The Sun ta wallafa cewa Akanmi ya ce:

“Ana umartar duk masu ruwa da tsaki da su dakatar da sayar da fom nan take har sai an yanke hukunci na ƙarshe kan shari’ar da ke gaban babbar kotun tarayya."

Tsagin Nafiu Bala ya yabawa kotu

Tsagin Nafiu Bala ya kuma yaba wa kotun koli bisa hukuncin da ta yanke ranar 30 ga Afirilu, 2026, inda ya bayyana hukuncin a matsayin wata babbar gudunmawa ga dimokuraɗiyya, kundin tsarin mulki da bin doka a tsarin siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsugune ba ta ƙare ba: kotu ta ɗage shari'ar rikicin shugabancin ADC a Abuja

Akanmi ya buƙaci mambobin haɗakar siyasar da ke cikin jam’iyyar da kuma tsagin Mark da su ajiye son rai na siyasa a gefe tare da haɗa kai da Nafiu Bala ke jagoranta domin tabbatar da haɗin kan jam’iyyar.

Shugabannin ADC a Najeriya
'Yan ADC bangaren David Mark a Najeriya. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A cewarsa, irin wannan haɗin kai na da muhimmanci wajen tabbatar da ADC ta shiga zaɓe mai zuwa da kuma tabbatar da samun sahihan ’yan takara a matakan jihohi da ƙananan hukumomi da ma gundumomi.

An dage sauraron shari'ar ADC

A wani labarin, mun kawo muku cewa zaman sauraron shari'ar ADC ya sake fuskantar tangarɗa bayan mai shari’a Emeka Nwite ya ɗage shari’ar ba tare da sanya wata rana ba.

Tun da farko dai shari’ar ta tsaya cak bayan David Mark ya shigar da ƙarar daukaka ƙara ta wucin-gadi, wadda daga baya ta kai har zuwa kotun koli.

A zaman kotun na ranar Juma’a, lauyan mai ƙara, Luka Musa Haruna ya shaida wa kotun cewa kotun koli ta yi watsi da daukaka karar wucin-gadi da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng