Sunaye: APC Ta Tantance Gwamnoni 12, Ta Amince Su Nemi Tazarce a Babban Zaben 2027

Sunaye: APC Ta Tantance Gwamnoni 12, Ta Amince Su Nemi Tazarce a Babban Zaben 2027

  • Gwamnonin APC sun fara gurfana a gaban kwamitin tantancewa na jam'iyyar APC yayin da shirye-shiryen zaben 2027 ke kara kankama
  • Kwamitin karkashin jagorancin shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya tantabce wasu daga cikin gwamnonin da yan takarar sanata
  • Da yake tsokaci kan tantancewar, Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu ya bayyana tsarin a matsayin mai sauƙi kuma mai kyau

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar APC ta fara tantance gwamnoni masu neman wa’adi na biyu da masu neman takarar Sanata gabanin zaɓukan fidda gwani na shekarar 2027.

Jam’iyyar ta fara aikin tantancewar ne a ranar Juma’a ƙarƙashin jagorancin shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.

Shugaban APC.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentwe Yilwatda a ofishinsa da ke hedkwatar jam'iyya, Abuja Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Leadership ta ruwaito cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamnoni a ranar 20 ga watan Mayu, yayin da na sanatoci zai gudana a ranar 18 ga watan Mayu, 2026.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Rikici ya barke tsakanin gwamnonin APC a taron Abuja, PGF ta dare gida 2

Gwamnoni 12 da jam'iyyar APC ta tantance

Daga cikin gwamnonin da suka bayyana domin tantancewa akwai gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago; gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia; da gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani.

Sauran sun haɗa da gwamnan Enugu, Peter Mbah; gwamnan Cross River, Bassey Otu; gwamnan Kebbi, Nasir Idris; da gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori.

Haka kuma akwai gwamnan Filato, Caleb Mutfwang; gwamnan Katsina, Dikko Radda; gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf; gwamnan Zamfara, Dauda Lawal; da gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu.

Gwamnonin da ke neman kujerar Sanata

APC ta tantance wadannan gwamnoni kuma ta sahale masu su nemi tazarce a kan mulki a babban zaben 2027, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Waɗanda aka tantance domin neman tikitin Sanata sun haɗa da gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri; gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya; da gwamnan Ogun, Dapo Abiodun.

Peter Mbah ya yaba wa tsarin APC

Da yake magana bayan tantancewarsa, gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya bayyana tsarin a matsayin mai sauƙi kuma mai kyau, yana mai cewa hakan ya nuna yadda APC ke da tsari mai inganci.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi garambawul a majalisar zartarwa da kwamishinoni 2 suka ajiye aiki

Ya ce:

“Mun yi alƙawarin ci gaba da kare ƙimar jam’iyyarmu tare da isar da saƙon ayyukan gwamnati ga ‘yan Najeriya a kowane yanki na ƙasa.”

Gwamna Mbah ya ƙara da cewa APC na zama abin koyi wajen tsara jam’iyya a Afirka.

Gwamnonin APC.
Gwamnanonin jam'iyyar APC yayin ganawa da manema labarai bayan kammala taro a Abuja Hoto: Hope Uzodinma
Source: Twitter

Da aka tambaye shi ko APC a Enugu za ta yi amfani da tsarin maslaha wajen fitar da ‘yan takara, sai ya ce:

“Mun saba gudanar da al’amura cikin haɗin kai kamar ‘yan’uwa, kuma hakan za mu ci gaba da yi.”

Rikici ya barke tsakanin gwamnonin APC

A wani labarin, kun ji cewa wani babban rikicin shugabanci ya ɓalle a cikin ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC (PGF), inda gwamnonin suka dare zuwa gida biyu.

Gwamnan Imo kuma shugaban ƙungiyar PGF, Hope Uzodimma, ya jaddada cewa shi ne har yanzu yake jagorancin PGF tare da mataimakinsa, Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna.

Amma wasu rahotanni sun nuna cewa wani babban ɓangare na gwamnonin ya janye goyon bayansa ga Hope Uzodimma, tare da zabar sababbin shugabanni.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262