Yaron Atiku Abubakar Ya Sayi Fam a ADC, Zai Nemi Takarar Sanata a Adamawa
- Ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Adamu Atiku, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar sanatan Adamawa ta Kudu a 2027
- Adamu ya ce ya yanke shawarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma goyon bayan al’umma domin ci gaban al'umma
- Ya bayyana cewa tafiyar tasa ta siyasa za ta mayar da hankali kan haɗin kai, ci gaba da wakilci mai inganci yayin da jama'a ke neman wakilci na gari
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Adamawa – Adamu Atiku, ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar sanatan Adamawa ta Kudu a babban zaɓen shekarar 2027 ƙarƙashin jam’iyyar ADC.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, tsohon kwamishinan ayyuka da bunƙasa makamashi na jihar Adamawa ya ce ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazari da shawarwari.

Source: Twitter
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa ya zauna da masu ruwa da tsaki da ke yankin kafin a kai ka cimma matsaya kan neman takarar.
'Dan Atiku Abubakar zai nemi takara
Jaridar Punch ta ce Adamu Atiku ya tabbatar da cewa ya shafe watanni yana nazari game da fitowa takarar Sanata a yankinsa.
Ya ce:
"Bayan watanni na tattaunawa mai faɗi, nazari da samun ƙarfafawa daga al’umma, masu ruwa da tsaki, magoya baya da sauran mutanen kirki daga Adamawa ta Kudu, na yanke shawarar amsa kiran yin hidima tare da shiga takarar kujerar sanatan Adamawa ta Kudu.”
Adamu ya ƙara da cewa tun da farko ya zaɓi yin shiru duk da matsin lambar da magoya bayansa ke yi masa, domin ya fi mayar da hankali kan yin shawarwari da nazari kafin yanke hukunci.
Ya bayyana cewa irin amincewa da goyon bayan da jama’a suka nuna masa ya ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen shiga takarar.
Adamu Atiku ya sayi fam din jam'iyyar ADC
Adamu Atiku ya kuma bayyana cewa ya riga ya karɓi fam ɗin tsayawa takara, yana mai cewa hakan ne ya zama farkon tafiyarsa ta neman kujerar sanatan yankin.

Source: Twitter
A cewarsa:
“Jiya na karɓi fam ɗin tsayawa takara a hukumance, wanda hakan ya nuna fara wannan tafiya tare da jajircewata wajen yi wa al’ummar Adamawa ta Kudu hidima.”
Ya bayyana wannan yunƙuri a matsayin tafiyar da jama’a suka assasa domin samar da wakilci mai ma’ana, haɗin kai da ci gaba a yankin.
A kalamansa:
“Wannan tafiya ta jama’a ce kuma tana tafiya ne bisa muradinmu na samun wakilci mai amfani, haɗin kai da ci gaba a faɗin Adamawa ta Kudu.”
Sanarwar ta zo ne makonni kaɗan bayan Adamu ya yi murabus daga majalisar gwamnatin Adamawa karkashin Ahmadu Fintiri, bayan gwamnan ya fice daga jam’iyyarsa tare da komawa jam’iyyar APC mai mulki.
Yaron Atiku ya bar gwamnatin Adamawa
A baya, kun ji cewa Alhaji Adamu Atiku ya sanar da murabus daga mukamin Kwamishinan Ayyuka da Ci gaban Makamashi na jihar Adamawa.
Adamu Atiku, wanda dan tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ne ya ajiye mukaminsa bayan Ahmadu Fintiri ya koma jam'iyya mai mulki ta APC.
Ya gode wa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa amincewa da goyon bayan da ya ba shi har ya shekara kusan bakwai yana hidima a gwamnatinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


