Tambuwal Ya Yi Dattaku, Ya Hakura da Takarar Sanata ga Tsohon Kwamishina
- Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya nuna dattaku a jihar Sokoto yayin fitar da ƴan takara a jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya
- Tambuwal ya janye daga takarar kujerar Sanatan Sokoto ta Kudu a karkashin ADC domin bai wa tsohon kwamishina
- Jam’iyyar ADC ta ce Tambuwal ya dauki matakin ne domin tabbatar da hadin kai, zaman lafiya da karfafa dimokuradiyya cikin gida gabanin zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya janye daga takarar kujerar Sanatan Sokoto ta Kudu.
Tambuwal wanda shi ne jagoran jam'iyyar a Sokoto ya hakura da takarar sanata a karkashin ADC mai adawa a Najeriya.

Source: Twitter
Rahoton Punch ya ce Tambuwal ya janye tare da mika tikitin ga tsohon kwamishinan kudi, Faruk Malami-Yabo.
Tambuwal ya janye takarar sanata a ADC
Rahotanni sun nuna cewa Tambuwal, wanda ake kallon jagoran ADC a Sokoto, ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da rashin jituwa kan zaben ‘yan takara gabanin babban zaben 2027.
Sakataren yada labarai na ADC a Sokoto, Lamir Aminu, ya tabbatar da hakan yayin hira ta wayar tarho, inda ya ce Tambuwal ya sadaukar da burinsa domin zaman lafiya.
Ya ce:
“Sanata Tambuwal ya hakura da tikitin ne domin karfafa hadin kai da dimokuradiyya a cikin gida a jam’iyyar tare da tabbatar da zaman lafiya.”

Source: Original
ADC za ta ba matasa dama
A cewarsa, shugabannin jam'iyyar ADC a Sokoto sun kuduri aniyar bai wa matasa damar tsayawa takara, yana mai cewa matakin ya dace da manufar jam’iyyar ta gina sababbin shugabanni.
Lamir Aminu ya kara da cewa yawancin tikitin takarar kujerun majalisar wakilai na jam’iyyar a Sokoto an bai wa matasa masu tasowa domin kara musu damar jagoranci.
Lamarin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da sauya sheka da sake tsara siyasa a cikin ADC a Sokoto kafin zaben shekarar 2027 da za a gudanar ranar 20 ga Fabrairun 2027.
A wani bangaren kuma, jigo a ADC, Faruku Umar Fada, ya zama dan takarar jam’iyyar na mazabar tarayya ta Sokoto ta Arewa da Sokoto ta Kudu.
An sanar da fitowarsa a safiyar Juma’a yayin da harkokin siyasa suka fara daukar zafi a jihar kafin gudanar da zabukan shekarar 2027, cewar Daily Post.
Magoya bayan jam’iyyar sun bayyana Fada a matsayin dan siyasa mai kusanci da jama’a wanda ke da gagarumar goyon baya a fadin mazabar da yake son wakilta.
Na kusa da Tambuwal ya samu tikitin takara
An ji cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC domin zaɓen 2027 da ake tunkara.
Ɗan siyasar ya gode wa Aminu Waziri Tambuwal da sauran shugabanni, matasa, mata da magoya baya bisa goyon bayan da suka nuna masa wajen wannan tafiyar siyasa.
Ya ce sabon yunkurin ADC zai kawo shugabanci nagari, haɗin kai da manufofin ci gaban jama’a yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara ƙamari.
Asali: Legit.ng

