'Najeriya ba Ta Rago ba Ce': Malami Ya Gargadi Jonathan kan Takara

'Najeriya ba Ta Rago ba Ce': Malami Ya Gargadi Jonathan kan Takara

  • Fasto Elijah Ayodele ya gargadi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan game da takarar zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Ayodele ya gargadi Jonathan da ya yi taka-tsantsan kan batun tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027
  • Malamin cocin ya ce takarar Jonathan za ta girgiza APC tare da sauya tsarin siyasar Najeriya, amma ya nuna cewa tafiyar ba za ta kasance mai sauki ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya gargadi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Malamin ya bukaci Jonathan da ya yi taka-tsantsan game da batun tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Fasto Ayodele ya gargadi Jonathan
Fasto Elijah Ayodele yayin huduba a coci. Hoto: Elijah Babatunde Ayodele.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, ya fitar, cewar Tribune.

Matasa sun bukaci Jonathan ya tsaya takara

Kara karanta wannan

Jonathan ya kalubalanci wanda ya nemi hana shi fitowa takarar shugaban kasa a 2027

Wannan gargadi na zuwa ne bayan wasu matasa da magoya baya sun kai ziyara ga Jonathan domin rokon sa ya fito takarar shugaban kasa a babban zaben da ke tafe.

Goodluck Jonathan ya yi magana game da yiwuwar tsayawa takara a zaben shekarar 2027.

Jonathan ya yi karin haske ne yayin da matasan da suka bukaci ya tsaya takarar shugaban kasa suka kai masa ziyara a gidansa a Abuja.

Ya bukaci matasan Najeriya su ci gaba da neman sahihin zabe na gaskiya, yana mai cewa dimokuradiyya tana bunkasa ne idan jama'a sun taka rawa.

Fasto ya shawarci Jonathan kan takara a 2027
Fasto Elijah Ayodele da Goodluck Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan, Elijah Babatunde Ayodele.
Source: Facebook

Fasto Ayodele ya gargadi Jonathan

Ayodele ya ce duk da cewa Jonathan zai iya kawo sauyi a siyasar Najeriya, ya kamata ya kula ka da takarar ta bata masa suna, cewar Daily Post.

Ya ce:

"Jonathan zai dace da sake tsayawa takara a zabe, amma tabbas zai iya rasa kimarsa, zai bata sunansa."

Malamin cocin ya ce idan Jonathan ya yanke shawarar shiga takarar, hakan zai sanya duk sauran ‘yan takara ciki har da Bola Tinubu cikin matsin lamba mai tsanani.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kungiyar Obidient ta canza suna, ta kori Peter Obi da Yunusa Tanko

Ya kuma bayyana cewa Jonathan na nuna tsoro da rashin yanke hukunci kan lamarin, amma ya bukace shi da ya zama mai jarumtaka idan har da gaske yana son shiga takarar.

Ayodele ya ce tafiyar siyasa irin wannan ba ta masu raunin zuciya ba ce, saboda haka Jonathan dole ne ya shirya fuskantar kalubale masu yawa idan ya shiga fafatawar.

Haka kuma, faston ya yi hasashen cewa Jonathan zai samu goyon baya daga kasashen duniya da masu daukar nauyin siyasa idan ya yanke shawarar tsayawa takara.

Sai dai ya jaddada cewa duk da irin goyon bayan da zai iya samu, hanyar neman shugabancin kasar ba za ta kasance mai sauki ga Jonathan ba.

Jonathan ya kalubalanci yunkurin hana shi takara

Mun ba ku labarin cewa Goodluck Jonathan ya kalubalanci karar da aka shigar gaban babbar kotun tarayya da nufin hana shi fitowa takarar shugaban kasa a 2027.

Tsohon shugaban kasar ya nuna takaicinsa kan yadda aka shigar da karar duk da an taba yanke hukunci kan makamancin wannan batu.

Lauyansa, Cif Chris Uche (SAN), ne ya bayyana hakan a gaban Mai shari’a Peter Lifu na babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.