"Ba tare da Kashe Kowa ba": Obama Ya Fadi Yadda Ya Kulla Yarjejeniya da Iran

"Ba tare da Kashe Kowa ba": Obama Ya Fadi Yadda Ya Kulla Yarjejeniya da Iran

  • Tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ya yi magana kan yarjejeniyar da ya kulla da Iran a lokacin mulkinsa
  • Barack Obama ya bayyana cewa an kulla yarjejeniyar ne ba tare da harba makami ko kashe ran ko mutum guda ba
  • Tsohon shugaban na Amurka ya nuna muhimmancin amfani da diflomasiyya wajen tattaunawa da Iran kan shirinta na nukiliya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya bayyana muhimmancin amfani da diflomasiyya kan ƙasar Iran.

Barack Obama ya kafa hujja da yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015 a matsayin shaidar cewa za a iya takaita shirin Tehran ba tare da sake yin amfani da matakin soja ba.

Obama ya yi magana kan yarjejeniya da Iran
Tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Jaridar The Hill ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 14 ga watan Mayun 2026 cewa Obama ya bayyana hakan ne a shirin 'The Late Show”, Stephen Colbert, yayin wata tattaunawa a watan jiya.

Kara karanta wannan

"Ba dai a matsayin rauni ba," Gwamna Radda ya kafa sharadin sulhu da 'yan bindiga

Me Obama ya ce kan yarjejeniya da Iran?

“Mun yi ƙoƙarin tattauna yarjejeniyar diflomasiyya wadda za ta fitar da sinadarin uranium da aka inganta daga Iran, wadda za ta tabbatar da cewa ba za su iya kera makamin nukiliya ba tare da mun sani ba. kuma akwai hanyoyin da aka tsara don tilastawa da kuma tabbatar da hakan."
“Kuma mun cimma hakan ba tare da mun harba makami mai linzami guda ɗaya ba."

- Barack Obama

Obama yana magana ne kan yarjejeniyar JCPOA, wata yarjejeniyar hadaka da aka tattauna lokacin wa'adinsa na biyu kan mulki da aka tsara ta don dakile shirin nukiliyar Iran, don musanya da dage takunkumai daga Amurka, Russia, China, Faransa, Burtaniya, da kuma Jamus.

Obama ya yi tunanin amfani da karfi

Tsohon shugaban ya tuno cewa gwamnatinsa ta auna batun yin amfani da ƙarfin soja da Tehran a wannan lokacin, amma ta zaɓi yin amfani da shi a matsayin “mataki na ƙarshe” bayan tattaunawar diflomasiyya, rahoton Firstpost ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

“Ainihin ra’ayina shi ne cewa Iran ba za ta iya zama ƙasa mai makamin nukiliya ba, domin gwamnatin da kanta mai kashe mutane ce, galibi ma ga mutanenta, tana da hannu a ta’addanci da ƙasa ke ɗaukar nauyi."
"Kuma tana da barazana ga Amurka da ƙawayenmu, don haka tunanin cewa za su mallaki makaman nukiliya zai kasance mai matuƙar hadari."
"Abin da kuma na yi amanna da shi shi ne, gwamnatin ba wai gaba ɗaya ba ta da hankali ba ce, suna da sha’awar rayuwa, kuma idan ka aiwatar da ƙarfin soja, mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba ne ke mutuwa.”

- Barack Obama

Obama ya tabo batun yarjejeniyar da ya kulla da Iran
Barack Obama, tsohon shugaban kasar Amurka Hoto: Earl Gibsons III
Source: Getty Images

An kwashe lokaci ana tattaunawa

Tattaunawar ta kasance mai tsayi da sarkakiya, amma daga ƙarshe, Iran ta amince da manyan takaitawa ga shirin nukiliyarta kuma ta buɗe wuraren ayyukanta ga masu sanya ido na ƙasa da ƙasa.

Yarjejeniyar ta buƙaci Iran da ta rage adadin sinadarin uranium ɗinta da kusan kashi 98 cikin 100.

“Babu wata muhawara kan cewa ko hakan ya yi aiki, kuma ba mu yi ba, ba mu kashe dandazon mutane ko mu rufe Mashigar Hormuz ba."

Kara karanta wannan

An zo wajen: Putin ya yi maganar lokacin kawo karshen yakin Rasha da Ukraine

- Barack Obama

Yarjejeniyar JCPOA ta ci gaba da aiki tun daga watan Janairun 2016 har sai lokacin da Shugaba Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar da kansa a lokacin mulkinsa na farko a shekarar 2018.

Amurka da Iran sun kasa cimma matsaya

A wani labarin kuma, kun ji cewa an kasa cimma matsaya tsakanin Amurka da Iran kan batun kawo karshen yakin da ake yi.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa tayin da Iran ta gabatar domin kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe makonni 10 ana yi a Gabas ta Tsakiya abin ƙi ne gaba ɗaya.

A cikin martanin nata, Iran ta buƙaci a biya ta diyya saboda yaƙin, a ba ta cikakken iko kan mashigar ruwa na Hormuz wanda ta cikin ƙasar ta ratsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng