Siyasar Arewa
Hukumar INEC a jihar Kebbi ta bayyana cewa APC da LP ne kadai jam'iyyun da suka cika sharuddan shiga zaben cike gurbi na majalisar dokoki a Zuru.
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya umarci jami'an da ya ba mukaman siyasa da su koma jam'iyyar APC cikin sa'o'i 48 ko ya kore su daga aiki.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa ya ga ‘ya’yansa sau uku kacal cikin kwanaki 55 bayan hawansa mulki saboda matsalar tsaro da ta addabi Borno.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa yana cikin jam'iyyar NDC tare da Peter Obi, Nasiru Gawuna da Aminu Abdulsalam Gwarzo. Ya ce za su yi aiki tare a 2027.
A labarin nan, za a ji cewa kungiyar Kwankwasiyya ta bayyana gaskiyar abin da ya faru bayan jam'iyyar NDC ta sauya sunayen wasu 'yan takara da Kwankwaso ya tsayar.
Tsohon shugaban DSS, Lawal Daura ya ƙalubalanci tsarin da ADC ta bi wajen fitar da ɗan takarar gwamna a Katsina tare da yin barazanar zuwa kotu idan ba a bi doka ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya tanka wa Babachir Lawal, ya ce tsohon sakataren gwamnatin Najeriya na neman raba kan yan Najeriya.
Jam’iyyar NDC da takarar haɗin gwiwar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na fuskantar turjiya daga wasu shugabanni da masu zaɓe a Arewacin Najeriya.
Mubarak Musa Dantori, wanda ya nemi takarar majalisar dokoki a karkashin ADC, ya fice daga jam’iyyar tare da komawa jam'iyyar PDP mai adawa a Gombe.
Siyasar Arewa
Samu kari