Ana Tsaka da Rikicin Siyasa, Surukin Sanata Goje Ya Yi Mubaya’a ga Gwamna Inuwa
- Surukin Sanata Danjuma Goje, Ibrahim Dasuki Waziri, ya yi wata ganawa da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a Gombe
- Dasuki Waziri ya yabawa gwamnatin Inuwa Yahaya kan ayyukan ci gaba, zaman lafiya da hada kan jama’a
- Wannan mataki na zuwa ne yayin da rikicin siyasa tsakanin Gwamna Inuwa da Sanata Goje ke kara kamari kan zaben 2027
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Honarabul Ibrahim Dasuki Jalo Waziri, surukin tsohon gwamnan jihar Gombe Sanata Muhammad Danjuma Goje ya gana da Gwamna Inuwa Yahaya.
Waziri ya sake bayyana biyayyarsa da goyon bayansa ga Gwamna Inuwa Yahaya duk matsalar siyasa da ke tsakanin gwamnan da surukinsa.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da Darakta Janar na harkokin yada labarai na gidan gwamnati, Isma’ila Uba Misilli ya fitar a shafin Facebook.
Dasuki Waziri, wanda ya auri Zainab Danjuma Goje, diya ta biyu ga Sanata Goje, ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa gwamnan a gidan gwamnati da ke Gombe ranar Litinin.
Tsohon kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu ya yabawa gwamnan bisa abin da ya kira manyan nasarori a bangaren gine-gine, zaman lafiya da shugabanci mai hada kan jama’a a fadin jihar.
An rawaito Dasuki na yabawa salon shugabancin Inuwa Yahaya, yana cewa hakan ya kara dankon zumunci a APC tare da kara wa jama’a kwarin gwiwa ga gwamnati.
Dasuki, wanda ya taba zama shugaban kungiyar kananan hukumomin Najeriya ALGON na kasa, ya ce ayyukan ci gaba da gwamnatin ta aiwatar sun amfani al’ummomi da dama a jihar.
A cewarsa, kokarin gwamnan wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba ya cancanci samun goyon bayan duk masu kishin jihar ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.
Ya ce:
“Muna alfahari da shugabancinka da ci gaban da aka samu a karkashin gwamnatinka. Kokarinka wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaba abin yabawa ne sosai."
Ya kuma tabbatar wa gwamnan da ci gaba da biyayyarsa tare da shirinsa na bada gudunmawa wajen tabbatar da hadin kai da kwanciyar hankali a APC da jihar Gombe baki daya.
A nasa bangaren, Gwamna Inuwa Yahaya ya gode da ziyarar, yana mai cewa hakan alama ce ta balagar siyasa, hadin kai da kishin ci gaban jihar.
Lamarin na zuwa ne yayin da harkokin siyasa ke kara daukar zafi gabanin babban zaben shekarar 2027 a jihar Gombe.
Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Inuwa Yahaya na cikin takun-saka da Sanata Goje kan yunkurin dan majalisar na komawa majalisar tarayya karo na biyar.
A wani taron sulhu da aka gudanar kwanan nan, gwamnan ya zabi DCP Mohammed Ahmed Deba mai ritaya a matsayin dan takarar sulhu na APC domin maye gurbin Goje a majalisar tarayya.
Goje ya yaba wa mulkin Tinubu
Mun ba ku labarin cewa Sanata Muhammad Danjuma Goje ya yabawa shugaba Bola Tinubu da majalisar tarayya bisa kokarinsu na yin shugabanci mai nagarta a kasa.
Tsohon gwamnan ya yi kira ga al’ummar ƙasa da a ci gaba da addu’a don samun nasarar shugabancin Tinubu da 'yan majalisa.
Sanata Goje ya ce majalisar dattawa ta 10 za ta ci gaba da aiki tare da bangaren zartarwa domin ganin an samu ci gaba mai ɗorewa.
Asali: Legit.ng

