Kwankwaso Ya Fito da Korafe Korafe kan Buhari game da Taimaka Masa a 2015

Kwankwaso Ya Fito da Korafe Korafe kan Buhari game da Taimaka Masa a 2015

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan yadda lamura suka gudana bayan sun taimakawa Muhammadu Buhari ya lashe zabe a 2015
  • Kwankwaso ya yi tsokaci kan mulkin wasu shugabannin Najeriya da suka hada da Olusegun Obasanjo, Umaru Musa Yar'adua da Goodluck Jonathan
  • Bayanan tsohon gwamnan Kano sun zo ne kwanaki kadan bayan ya koma jam'iyyar NDC tare da hada kai da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya ce shi da magoya bayansa ba su samu komai ba bayan sun taimaki Muhammdu Buhari ya yi nasara.

Ya ce sun samar da kusan ƙuri’u miliyan biyu domin taimaka wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya hau mulki a shekarar 2015, yana mai cewa wannan ne ya sa ya fara neman sauya sheka.

Kara karanta wannan

Duk da yana NDC, Kwankwaso ya tabo batun aiki tare da Atiku, ADC a 2027

Rabiu Musa Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso yayin wani taron siyasa a Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar Arise TV, inda ya yi magana kan irin sadaukarwar da ya yi wajen mara wa Buhari baya a zaɓen da ya kawo ƙarshen mulkin jam’iyyar PDP.

Korafin Kwankwaso kan Buhari

Yayin da yake bayani game da taimakon da ya yi wajen samun nasarar shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC a 2015, Kwankwaso ya ce:

“Na yi aiki tuƙuru sosai. Mun kawo kusan ƙuri’u miliyan 1.9, kusan miliyan 2. Amma a matsayinmu na ’yan siyasa, ba a girmama mu ba. Har ma mun saka rayuwarmu cikin haɗari a lokacin.
"Amma abin takaici, ba mu ga wata fa’ida ba ko dai gare mu da kanmu ko kuma yankunan da muke wakilta,”

Tsohon gwamnan Kano bai bayyana abin da yake tsammanin samu ba ko kuma ainihin abin da gwamnatin Buhari ta gaza yi ba.

Bayani kan wasu gwamnatoci

Kara karanta wannan

2027: Yadda 'yar Kwankwaso ta shawo kan shi game da hada kai da Obi

Punch ta wallafa cewa Kwankwaso ya yi bayani kan kowace gwamnati tun daga shekarar 1999 domin nuna dalilin da ya sa yake ganin yanzu ƙasar ta shirya domin samun sauyi na gaskiya.

Ya ce Olusegun Obasanjo ya yi iya ƙoƙarinsa, yayin da Umar Yar'Adua ya fuskanci matsalolin rashin lafiya mai tsanani, sannan mulkin Goodluck Jonathan ya gamu da rikici kan yarjejeniyar da ake cewa zai yi wa’adi ɗaya kacal.

“Dukkan mutane sun san akwai matsaloli a tattare da wannan gwamnati ma,”

In ji Rabiu Kwankwaso yana magana kan gwamnatin Bola Tinubu da ke ci a Najeriya a yau.

Rabiu Kwankwaso da Peter Obi
Peter Obi da Rabiu Kwankwaso bayan komawa NDC. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

Maganar 'yar Kwankwaso kan haduwa da Obi

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan yadda 'yar sa ta ba shi shawarar haduwa da Peter Obi.

Kwankwaso ya sanar da cewa tun a zaben shekarar 2023 'yar cikinsa ta rika neman ya hada kai da Peter Obi da ya yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke magana kan muhimmancin hadin kai a Najeriya bayan ya hada kai da Obi a jam'iyyar NDC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng