Sheikh Pantami Ya Fadi Abubuwa 4 da Ya Fi Sauran Masu Son Zama Gwamna a Gombe

Sheikh Pantami Ya Fadi Abubuwa 4 da Ya Fi Sauran Masu Son Zama Gwamna a Gombe

  • Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi karin bayani game da dalilan da suka sanya shi shiga neman tikitin takarar gwamna
  • A wata hira da aka yi da shi, Pantami ya bayyana cewa akwai wasu muhimman abubuwan da suka bambanta shi da sauran 'yan takara
  • Ya bayyana cewa a shirye ya ke wajen kawo cigaba mai dorewa a jihar matukar jam'iyyar APC ta tsayar da shi kuma ya lashe zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Tsohon ministan sadarwa a gwamnatin Muhammadu Buhari, Isa Ali Pantami ya bayyana cewa yana da kwarewar jagorantar jihar Gombe a matsayin gwamna.

Sheikh Pantami ya bayyana haka ne yayin da ya nuna kin amincewa da wanda gwamnan jihar ya nuna a matsayin wanda ya ke so ya gaje shi a 2027.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya ba da mamaki, ya ki tsayawa takarar sanata a 2027

Sheikh Is Ali Pantami
Lokacin da Sheikh Isa Ali Pantami wa'azi a Abuja. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da Tashar Trust TV, Pantami ya bayyana cewa akwai wasu abubuwa akalla hudu da suka bambanta shi da sauran masu neman tikitin APC a Gombe.

Me Isa Pantami ya fi masu son takara?

A hirar da ya yi, Pantami ya bayyana cewa yana da wasu abubuwan da sun bambanta shi da sauran masu son samun tikitin APC a Gombe.

Abubuwan da ya ambata su ne:

1. Kwarewa a bangarori da dama

Sheikh Pantami ya bayyana cewa shi kwararre ne a bangarori da dama, yana ishara da cewa bayan zama malamin addini, shi cikakken dan boko ne.

Kasancewar babu wanda ya hada abubuwan biyu a cikin masu neman tikitin, Pantami ya ce hakan zai ba shi damar kallon lamura ta hanyoyi daban-daban domin kawo sauyi a jihar.

2. Alaka da yankunan duniya

A bayanan da ya yi, tsohon ministan ya sanar da cewa a yanzu haka sunan Pantami ya karade kusan ko ina a duniya, inda ya ce an san garin Pantami a Gombe, Najeriya, Afrika da duniya baki daya.

Kara karanta wannan

Jami'in gwamnatin Tinubu ya goyi bayan takarar Pantami a Gombe

Ya bayyana cewa hakan zai ba shi dama wajen alaka da kasashe domin hada kai, jawo masu zuba jari, samar da tallafin karatu da sauransu.

Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami yayin wani taron APC. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

3. Kokarin da ya yi a baya

Pantami ya bayyana cewa idan aka duba ayyukan da ya yi a lokacin da ya ke shugaban NITDA da ministan sadarwa za a tabbatar da nagartarsa.

Ya ce ya zartar da ayyuka da dama domin kawo cigaba a dukkan yankunan Najeriya, musamman jihar Gombe da ya fito daga cikinta.

4. Karbuwa da ya yi cikin jama'a

Cikin dalilan da Pantami ya kawo ya bayyana cewa ya samu karbuwa a cikin al'ummar Najeriya, musamman jihar Gombe, wanda hakan wata dama ce ta nuna cewa ya bambanta da sauran mutane.

A kan haka ya sanar da cewa yana cewa yana shirye domin tunkarar zaben fitar da gwani da jam'iyyar APC za ta yi a jihar Gombe.

Legit ta tattauna da Aminu Isa

Biyo bayan kalaman Pantami, Legit ta tattauna da wani na hannun daman Jamilu Gwamna domin jin ko gwaninsu yana da abubuwan da suka nuna ya fi cancanta.

Kara karanta wannan

Malami ya yi abin kunya, kotu ta kama shi da laifin dirka wa 'yan mata ciki a Kwara

Aminu ya ce:

"Mai gidan mu kwararre ne. Ya yi karatu a jami'ar Ahmadu Bello, inda ya zama Akanta. Saboda haka yana da kwarewa a fanninsa kuma hakan zai taimaka masa.
"Mutum ne da ya samar da ayyuka sosai ga al'umma, wannan ya nuna bai manta da jama'a ba a lokacin da ya samu dama."

MURIC ta goyi bayan matsayarma Pantami

A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar MURIC da ke rajin kare hakkin al'ummar Musulmi ta nuna goyon bayan ga Sheikh Isa Ali Pantami.

Shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya bayyana cewa dole a yi wa Sheikh Pantami adalci wajen zaben fitar da gwani da za a yi a APC.

MURIC ta yi magana ne bayan Sheikh Pantami ya yi watsi da matsayar gwamnan Gombe kan cewa Jamilu Gwamna ne zai gaje shi a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng