Hayaniya Ta Kaure kan Rabon Lasisin Shigo da Fetur a Najeriya
- 'Yan kasuwar mai sun zargi NMDPRA da bai wa kamfanoni iri ɗaya lasisin shigo da mai akai-akai a 2026 tare da nuna wariyar launin fata
- Kungiyar yan kasuwa ta DAPPMAN ta ce hakan na tauye gasa tare da ware sauran kamfanonin da suka cancanci shigo da man fetur a kasar nan
- Sai dai hukumar gwamnati mai kula da daidaiton farashin na NMDPRA ta yi martani ga zargin cewa ta na nuna wariya wurin bayar da lasisi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Tsakiya da ta Ƙasa (NMDPRA) ta gamu da fushin ƙungiyoyin 'yan kasuwar man fetur.
Kungiyoyin sun zargi hukumar da ba wa wasu tsirarun kamfanoni lasisin shigo da mai, lamarin da suka ce yana rage gaskiya da adalci a kasuwar man fetur da aka buɗe wa gasa.

Kara karanta wannan
An yi wa dan APC mai tallata Tinubu jina jina, za a farauci wadanda suka daka shi

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa batun ya fito ne a zaman tattaunawa da Kwamitin Majalisar Wakilai kan Albarkatun Man Fetur (Downstream) ya shirya, inda ƙungiyoyin DAPPMAN, IPMAN da MEMAN suka gabatar da matsalolin da ke addabar harkar.
Yan kasuwar man fetur sun fusata
Rahoton ya ce kungiyar DAPPMAN ta ce lasisin shigo da mai na zangon farko, na biyu da na uku na shekarar 2026 ya fi komawa hannun wasu kamfanoni, yayin da aka bar wasu kamfanonin da suka cika sharuɗɗa a baya.
Sakataren zartarwa na DAPPMAN, Olufemi Adewole, ya zargi NMDPRA da rashin tabbatar da adalci wajen rabon lasisin.
Ya ce:
"Kamfanoni iri ɗaya ne suka samu lasisin shigo da mai a zangon farko, na biyu da na uku na shekarar 2026, tamkar babu sauran masu cancanta. Wannan ba abin karɓa ba ne."
A cewarsa, tsarin bai wa kamfanoni lasisi ya kamata ya kasance bisa adalci da damar bai ɗaya, musamman a lokacin da gwamnati ke ƙarfafa kasuwar man fetur mai cikakken 'yanci.
Koken yan kasuwa kan NMDPRA
Ƙungiyar ta ce bayanan da ta samu daga NMDPRA sun nuna cewa aƙalla ma'ajiyar man fetur 72 cikin 154 da aka ba lasisi ba su yi ciniki sosai a shekarar da ta gabata.
Haka kuma ta yi korafin caji iri biyu a tashoshin jiragen ruwa da kuma ci gaba da lissafa wasu hada-hadar man fetur a farashin Dala duk da umarnin gwamnatin tarayya na rage amfani da kuɗin waje a harkokin cikin gida.

Source: Twitter
Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Albarkatun Man Fetur, Hon. Ikenga Ugochinyere, ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa za a binciki zargin.
Ya ce za a gayyaci jami'an NMDPRA domin su bayyana ƙa'idodin da suka bi wajen bayar da lasisin shigo da man fetur a Najeriya.
An rage farashin man fetur a Najeriya
A baya, mun kawo labarin cewa masu sayar da man fetur sun rage farashin fetur a manyan matatun ajiya da ke Legas, Warri, Fatakwal da Calabar, lamarin da ake ganin zai iya jawo saukin farashi a kasa.
Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan dillalai sun rage farashi da har N23 kan kowace lita domin jawo karin kwastomomi a yayin da masu amfani da ababen hawa a sassan kasar ke kuka kan lamarin.
Masana sun bayyana cewa karin tace man fetur a gida da kuma gasa tsakanin 'yan kasuwa ne suka haddasa saukar farashin yayin da ake samun hauhawar farashi tun bayan fara yakin Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng

