Uba Sani zai Ajiye Muslim Muslim, zai Dauki Mataimaki Kirista a Kaduna
- Rahotanni sun nuna gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yanke shawarar zaɓar Kirista daga Kudancin Kaduna a matsayin mataimakinsa
- Ana ganin matakin zai kawo daidaito tsakanin addinai, sabanin tsarin tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi amfani da shi a zaɓen 2019
- Majiyoyi sun ce gwamnan bai bayyana sunan wanda zai zaɓa ba tukuna saboda gudun rikice-rikice da matsin lamba daga 'yan siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kaduna – Yayin da wa'adin miƙa sunayen 'yan takara da mataimakansu ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ke ƙaratowa, rahotanni sun nuna cewa an fara maganar mataimakin gwamna a Kaduna.
Wani rahoto ya nuna cewa Sanata Uba Sani, ya yanke shawarar zaɓar Kirista daga yankin Kudancin Kaduna a matsayin mataimakinsa a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa matakin na nufin komawa tsarin daidaita addinai a tikitin gwamna, sabanin abin da tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, ya yi a 2019 lokacin da ya zaɓi Musulma a matsayin mataimakiyarsa.
Uba Sani zai ajiye Muslim Musim
Majiyoyi daga gidan gwamnatin Kaduna sun bayyana cewa gwamnan ya yi dogon nazari kan batutuwan shekaru, jinsi, yanki da kuma addini kafin ya yanke hukuncin cewa aƙalla ya kamata a samu daidaito ta fuskar yanki da addini.
A cewar wata majiya:
"Gwamnan ya riga ya yanke shawara cewa domin adalci da haɗin kai, tikitinsa zai kasance mai daidaiton addini. Ko da ba za a iya daidaita sauran fannoni ba, aƙalla yanki da addini za su samu kulawa."
Majiyar ta ƙara da cewa Uba Sani ya ga ya dace Kudancin Kaduna ya ci gaba da riƙe kujerar mataimakin gwamna, amma a wannan karon ta hannun ɗan takara Kirista.
Waye ake hasashen za a zaɓa?
Rahoton Trust Radio ya ce gwamnan na ci gaba da tantance sunayen mutanen da ke gabansa kafin ya sanar da wanda ya zaɓa a hukumance.
Daga cikin waɗanda ake cewa suna cikin jerin akwai Kwamishinan Shari'a na jihar, James Kanyip, Shugabar Ma'aikatan Gwamnatin Jihar, Jummai Bako, da Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Kaduna (KADIRS), Jerry Adams.

Source: Twitter
Sai dai kakakin gwamnan, Malam Ibraheem Musa, ya ƙi tabbatar da rahoton, yana mai cewa lokaci zai yi da za a bayyana komai ga jama'a.
Tasirin matakin kan siyasar Kaduna
Masana siyasa na ganin idan Uba Sani ya tabbatar da zaɓar Kirista daga Kudancin Kaduna, hakan na iya ƙarfafa APC a yankin.
Rahoton ya kuma nuna cewa ɗan takarar gwamna na jam'iyyar ADC, Malam Isa Ashiru Kudan, ya riga ya zaɓi Irmiya Kantyok, wanda Kirista ne daga Kudancin Kaduna, a matsayin mataimakinsa.
Ana kuma cewa irin wannan tsari ya kasance yana ba Ashiru Kudan gagarumin goyon baya daga yankin a zaɓukan da suka gabata.
PFN ta soki Musulm Muslim
A wani labarin, mun ruwaito cewa ƙungiyar PFN ta bayyana cewa ba ta goyon bayan tsarin tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓukan Najeriya.
PFN ta ce Najeriya ƙasa ce mai addinai da ƙabilu daban-daban, don haka ya kamata shugabanni su riƙa nuna daidaito wajen zaɓen 'yan takara da mataimakansu.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne bayan jam'iyyar APC ta amince da tikitin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima a 2027.
Asali: Legit.ng


