'Dan Shekara 18 Ya Kafa Tarihi a Matsayin Farfesa Mafi Ƙarancin Shekaru a Funiya
- Nathan Thomas ya zama farfesa mafi ƙarancin shekaru a duniya bayan ya fara koyarwa yana da shekaru 18 kacal a kwalejin Miami Dade
- Matashin ya kammala digirin farko da na biyu a fannin Injiniyan Lantarki kafin ya fara aiki, abin da ya sa ya shiga kundin tarihin duniya
- Yanzu aka dai Nathan na koyarwa tare da karantar digirin lauya, yana shirin ƙwarewa a dokokin kare haƙƙin fasaha da kirkire-kirkire
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Amurka - A lokacin da ɗalibai matasa suka shiga ajin koyon shirye-shiryen kwamfuta a Miami Dade College a watan Agustan 2023, sun yi mamakin ganin cewa wanda zai koya musu darasin yana kusan shekarunsu.
Duk da haka, Nathan Thomas ya tsaya a gaban ajin cikin ƙwarewa, yana koyar da darussan da ya kware a kansu tun yana ƙarami.

Source: UGC
Tsarin karatun dan shekara Nathan Thomas
Wannan na kunshe ne a cikin rahoton da aka wallafa a shafin kundin tarihi na duniya, watau Guinness World Records.
Nathan, wanda aka haifa a ranar 9 ga Satumba, 2004 a Amurka, ya fara shiga kwalejin Miami Dade tun yana da shekara 10 ta hanyar tsarin haɗa karatun sakandare da jami'a.
Daga baya ya koma jami'ar kasa da kasa ta Florida yana da shekara 14 domin ci gaba da karatunsa.
Tun kafin ya kai shekarun da mafi yawan matasa ke shiga jami'a, Nathan ya riga ya samu digirin farko da na biyu a fannin Injiniyan Lantarki, dukkansu tare da sakamakon girmamawa.
Nathan ya kafa sabon tarihi a duniya
Bayan kammala karatunsa, Nathan ya koma Miami Dade College a matsayin malami. A ranar da ya fara koyarwa yana da shekaru 18 da kwanaki 346, ya zama farfesa mafi ƙarancin shekaru a duniya, inda ya karya tarihin da Colin Maclaurin ya riƙe tsawon fiye da shekaru 300.
Haka kuma, ya fi Alia Sabur ƙarancin shekaru da kwanaki 16 lokacin da ita ma ta kafa tarihin farfesa mafi ƙarancin shekaru a shekarar 2008.
Shekaru ba su hana koyarwa ba
Nathan ya ce bai taɓa damuwa da kasancewarsa ƙarami ba, domin manufar kowa a aji ita ce koyon ilimi.
“Da zarar ka shiga aji, duk wanda yake wurin ya zo ne domin ya koya. Shekaru ba su da muhimmanci idan ana maganar ilimi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne taimaka wa ɗalibai su fahimci darasi da kuma ƙarfafa masu ƙoƙarin koyo.
Nathan ya bayyana cewa tun yana yaro yake son karatu, musamman fannin kimiyya da fasaha (STEM), domin lissafi shi ne darasin da ya fi fahimta. Kasancewar iyayensa injiniyoyi ya taimaka wajen gina sha'awarsa tun yana ƙarami.

Source: UGC
Yanzu yana karantar lauya
Bayan kafa tarihi a fannin koyarwa, Nathan bai tsaya ba. Yanzu yana koyar da darussa ta yanar gizo tare da karantar digirin lauya a jami'ar koyon lauyanci ta Miami, inda yake sa ran kammala karatunsa a shekarar 2028.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: An hango yadda malaman makaranta masu yawa za su ajiye aiki a Borno
Ya bayyana cewa burinsa shi ne ya ƙware a fannin dokokin kare haƙƙin fasaha da kirkire-kirkire, domin ya haɗa ilimin injiniya da na shari'a wajen taimaka wa masu ƙirƙira da masana fasaha.
Mai tuka baro ya zama farfesa
A wani labari, mun ruwaito cewa, Nicholas Asogwa, lakcara a jami'ar UNN, ya ba da labarin yadda ya fita daga talauci ya zama farfesa da taimakon kwastamominsa biyu da suka dauki nauyin karatunsa.
Asogwa yana sana'ar tura baro da gyaran takalma a jami'ar kafin Nkechi Ohanuka ta siya masa takardar JAMB sannan Proscovia Ndoboli ta biya masa kudin makarantarsa na farko.
Asogwa ya sake haduwa da wadanda suka taimaka masa a 2013 sannan ya gode masu da iyayensa kan gudunmawa da karfafa masa gwiwa da suka yi.
Asali: Legit.ng

