Sabani Ya Bulla APC bayan Kifar da Mutum 150 yayin Tantance Masu Son Takara
- Ana cigaba da samun korafi a jam'iyyar APC yayin da aka kammala sayar da fom ana tantance masu neman takara a zaben 2027 da ke tafe
- Kwamitin tantance masu sha'awar takara a matakai daban-daban ya zubar da mutane akalla 150 da suka riga sauka saye fom a jihohi
- Wasu 'yan jam'iyyar APC sun sauya sheka yayin da wasu daga cikinsu suka kalubalanci matakan da gwamnonin jihohi suka dauka kan takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Korafe-korafe, zanga-zanga, barazanar shari’a da zargin kakaba ’yan takara sun biyo bayan aikin tantance masu neman takara da jam’iyya mai mulki ta APC ke gudanarwa a jihohi.
Lamarin ya bayyana ƙarin rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar kan amfani da tsarin cimma matsaya da kuma cire masu neman takarar zaben 2027.

Source: Facebook
Rahoton da jaridar Punch ta fitar ya nuna cewa wasu masu neman takara da suka fusata a jihohin Taraba, Kano, Jigawa, Anambra, Benue, Kogi, Kaduna, Ebonyi, Rivers da Plateau na shirin kai kara kotu.
Riciki kan tantance 'yan APC
Aikin tantancewar wani ɓangare ne na tsarin APC na ƙasa baki ɗaya domin rage yawan masu neman takara kafin zaɓen fidda gwani.
Sai dai aikin ya riga ya haddasa ce-ce-ku-ce a jihohi da dama, inda ake sa ran waɗanda aka cire za su nemi adalci ta hannun kwamitocin ɗaukaka ƙara.
A wasu jihohin, an riga an fara zanga-zanga, yayin da a wasu kuma masu ruwa da tsaki a jam’iyyar suka yi gargadin cewa yunƙurin kakaba ’yan takara na iya haddasa ficewa daga jam’iyyar.
Rikicin APC a jihar Taraba
A jihar Taraba, amincewa da ’yan majalisa masu ci, wanda aka ce masu ruwa da tsaki a jam’iyyar suka mara wa baya bayan aikin tantancewar, ya jawo sabani.
Wani jigo daga ƙaramar hukumar Karim Lamido, Paul Penuel ya bayyana ba za su goyi bayan sanatan da aka tsayar musu domin ya yi tazarce ba.
Rikicin 'yan takarar APC a Kano
A jihar Kano, an cire aƙalla masu neman takara 20 da ke neman tikitin Sanata da Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin Jiha duk da yarjejeniyar cimma matsaya da aka yi tun farko.
Daga cikin waɗanda lamarin ya shafa akwai tsohon shugaban ma’aikata, Usman Bala; tsohon ɗan majalisa, Sha’aban Sharada; Muhammad Zango; Danyaro Yakasai; Abbas Abbas; Shehu Driver da A.A. Zaura.
Sai dai sakataren yaɗa labarai na APC a Kano, Auwal Soja ya tabbatar da cewa masu neman takara shida a Kano ta Tsakiya sun janye wa tsohon gwamna Ibrahim Shekarau baya bayan wani babban taron sulhu.
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a Facebook cewa an yi sulhu tsakanin Sanata Barau Jibrin da A.A Zaura.

Source: Facebook
Rikicin APC a Jigagwa, Benue
A jihar Jigawa, rikicin jam'iyyar APC da ya biyo bayan aikin tantancewar ya kai ga murabus da sauya sheƙa zuwa jam'iyyun adawa.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali a Filato, ƴan bindiga sun kashe gomman mutane a sabon hari
Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa, Isah Idris ya fice daga APC bayan an cire shi daga takara aka maye gurbinsa da wani.
A cikin wasiƙar murabus ɗinsa, Idris ya nuna takaicinsa kan abin da ya bayyana a matsayin barin jam’iyyar daga manufofin da aka kafa ta a kai.
A jihar Benue, an rawaito cewa an cire kusan masu neman takara 40 yayin tantance masu neman shiga majalisar dokokin jiha da aka gudanar a Makurdi.
An riga an samu rashin jin daɗi tsakanin magoya bayan waɗanda aka cire, inda suka zargi jam’iyyar da karya tsarin rabon mukamai da kuma ware wasu ɓangarori daga wakilci.
A jihar Kogi, zanga-zanga da zargin mulkin kama-karya sun biyo bayan zargin cewa an raba fom ɗin takara ga waɗanda aka fi so kawai.
Korafin Pantami kan takara
A wani labarin, kun ji cewa tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa shi ya fi dacewa ya samu takarar gwamna karkashin APC a Gombe.
Pantami ya fadi wasu abubuwa hudu da ya ce sune suka bambanta shi da sauran 'yan siyasar jihar masu neman takarar gwamna a 2027.
Ya yi korafi ne bayan gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya nuna cewa Jamilu Isiyaku Gwamna ya ke fata ya gaje shi bayan kammala wa'adi na biyu.
Asali: Legit.ng

