APM Ta Ce Tinubu Ya Tara Malaman Addini Ya Sharara Masu Karya
- Jam'iyyar APM ta zargi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da yi wa limaman Katolika bayanan da ba su dace da halin da Najeriya ke ciki ba
- APM ta ce ikirarin da shugaban ya yi cewa tattalin arziki ya farfado da tsaro ya inganta ya saba da halin da 'yan Najeriya ke ciki a yau
- Jam'iyyar ta kalubalanci Tinubu da ya yi tafiya ta mota zuwa kowace jiha ko ya ziyarci kasuwa domin ya ji halin da jama'a ke ciki kafin zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Jam'iyyar APM ta caccaki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kalaman da ya yi wa limaman cocin Katolika dangane da tattalin arziki da tsaro a Najeriya.
Jam'iyyar ta ce ikirarin shugaban cewa tattalin arzikin kasar ya farfado kuma gwamnatinsa ta ceci Najeriya daga matsalar rashin tabbas bai dace da abin da miliyoyin 'yan Najeriya ke fuskanta ba.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa APM ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Abubakar Yusuf, ya fitar.
APM ta kalubalanci Tinubu
Jam'iyyar ta ce abin mamaki ne shugaban kasa ya yi irin wadannan kalamai ga manyan limaman Katolika da ke hulda da talakawa a kullum.
APM ta yi ikirarin cewa bayanai daga wasu cibiyoyi masu zaman kansu sun nuna cewa sama da 63% na 'yan Najeriya na rayuwa cikin talauci a shekarar 2026.
A cikin sanarwar, Leadership ta rahoto jam'iyyar ta ce:
"Yin irin wadannan ikirari ga limaman Katolika a lokacin da miliyoyin 'yan Najeriya ke kara fadawa cikin matsanancin talauci, yayin da 'yan ta'adda ke ci gaba da kashe mutane da sace su, babban raini ne ga limaman da kuma 'yan Najeriya baki daya."
Jam'iyyar ta kara da cewa karin farashin fetur ya janyo hauhawar kudin sufuri, kayan abinci, kudin makaranta, kula da lafiya, haya da sauran muhimman bukatun rayuwa.

Source: Facebook
APM ta soki Tinubu kan tsaro
Jam'iyyar ta kuma ce gwamnatin Tinubu ba ta dauki kwararan matakai wajen kawo karshen ta'addanci ba, sai dai tana ci gaba da yin alkawura.
Ta kalubalanci shugaban kasa da ya bar fadar shugaban kasa ya yi tafiya ta mota zuwa duk birnin da ya zaba ko kuma ya shiga kowace kasuwa domin ya gaya wa jama'a cewa rayuwarsu ta inganta.
Har ila yau, jam'iyyar ta bukaci masu ba shugaban kasa shawara su daina jefa shi cikin abin kunya da ikirarin nasarorin da ba su bayyana a idon jama'a ba.
ADC ta caccaki Bola Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar ADC ta soki shugaban kasa Bola Tinubu kan kalamansa na cewa a shirye yake ya yi gwagwarmayar siyasa.
Jam'iyyar ta ce ya kamata shugaban kasa ya fi mayar da hankali wajen yakar 'yan ta'adda maimakon fafatawa da jam'iyyun adawa.
ADC ta bayyana cewa hare-haren 'yan bindiga da ta'addanci na ci gaba da kara kamari a sassan Najeriya, yana mai cewa hakan ya kamata ya zama abin da zai yaka.
Asali: Legit.ng

