Yadda Iran Ta Zagaye, Ta Sayo Makaman Kariya na Miliyoyin Dala a China

Yadda Iran Ta Zagaye, Ta Sayo Makaman Kariya na Miliyoyin Dala a China

  • A yayin da Amurka ke ci gaba da kai wa wa Iran hari, kasar ta sayi wadansu manyan makamai da za su ba su kariya daga kasar China
  • Ana zargin yarjejeniyar ta kai ta Dala miliyan 60 zuwa 70, kuma ta ƙunshi makamai tsakanin 300 zuwa 400 da za su taimaka a yaki da Amurka
  • Sai dai kasar China ta musanta rahoton, yayin da Pakistan ta ce ba ta da hannu wajen jigilar makaman da ake zargin cewa China ta sayo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Iran - Daular Musulunci ta Iran na shirin karɓar kashin farko na makaman kariyar sararin samaniya masu ɗaukar kafa da aka ƙera a ƙasar China a cikin makwanni masu zuwa.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake kara musayar wuta tsakanin Iran da Amurka da wasu kasashe a Gabas ta Tsakiya domin kare kanta.

Kara karanta wannan

Iran: 'Ana kokarin goga mana kashin kaji kan harin Saudiyya'

Ana zargin Iran ta sayo makamai a China
Mojtaba Khamnei, shugaban kasar China Hoto: Getty
Source: Getty Images

Wadansu majiyoyi uku masu masaniya kan yarjejeniyar sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuter cewa tabbas an kulla wannan yarjejeniya.

Ana zargin Iran ta sayo makamai

BBC Hausa ta kawo labarin cewa majiyoyin sun bayyana cewa yarjejeniyar ta shafi sayen makaman kariyar sama masu ɗaukar kafa (MANPADS) tsakanin guda 300 zuwa 400. Daga cikin makaman akwai nau'ikan QW-12 da FN-16 da China ke ƙerawa.

Rahoton ya ce darajar yarjejeniyar ta kai tsakanin Dala miliyan 60 zuwa 70, kuma ana kallonta a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙoƙarin da Tehran ke yi na ƙarfafa kariyar sararin samaniyarta mai gajeren zango bayan watannin yaƙi da Amurka da Isra'ila.

A cewar majiyoyin, an rattaba hannu I yarjejeniyar ne da kamfanin Zhongqing Baoshang mai hedikwata a Hong Kong, wanda ake zargin ya taka matsayin mai shiga tsakani tsakanin Iran da kamfanin da zai samar da makaman daga China.

China ta musanta sayar wa Iran makamai

Kara karanta wannan

Akwai matsala: An hango yadda malaman makaranta masu yawa za su ajiye aiki a Borno

Majiyoyin sun nemi a sakaya sunayensu saboda muhimmancin batun, yayin da Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan rahoton ba.

Sai dai Ma'aikatar Harkokin Wajen China ta musanta labarin, tana mai cewa rahotannin ba su da tushe balle makama. Ta ƙara da cewa Sin ta ci gaba da taka rawa wajen ƙoƙarin samar da zaman lafiya da kawo ƙarshen rikici.

China ta karyata cewa an sayar wa Iran makamai
Shugaban kasar China, Xi Jinping Hoto: Getty
Source: Getty Images

Har ila yau, kamfanin Zhong Qing Bao Shang, wanda shi ne kamfanin iyaye na Zhongqing Baoshang, bai mayar da martani kan tambayar da aka yi masa ba.

Rahoton ya ce Iran na ƙoƙarin sake gina ƙarfin sojinta bayan watannin yaƙin da Amurka da Isra'ila suka kai hare-hare kan wuraren da ke da alaƙa da shirye-shiryenta na makamai masu linzami.

Iran ta gano masu taimakon Amurka

A baya, mun kawo labarin cewa Iran ta zargi wasu ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya da taimaka wa Amurka wajen kai hare-haren soji a kan ƙasarta tare da lalata muhimman bangarorin ci gaba a yankuna da dama.

Gwamnatin Tehran ta ce wasu ƙasashen sun ba dakarun Amurka damar amfani da yankunansu wajen kai hare-hare, sai dai Iran ta jaddada cewa har yanzu tana son kyakkyawar alaƙa da maƙwabtanta.

Iran ta kara da cewa akwai dangantaka mai ƙarfi da muradun bai ɗaya tsakanin Iran da ƙasashen yankin Tekun Fasha, waɗanda za su iya zama tubalin gina amincewa da haɗin kai da zai kawo ci gaba da yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng