'An Dauko Hanyar Hana Tinubu Tazarce,' Matasan Arewa Sun Yi Gargadi

'An Dauko Hanyar Hana Tinubu Tazarce,' Matasan Arewa Sun Yi Gargadi

  • Wata kungiyar matasa a Arewacin Najeriya ta yi gargadi kan zagin tsara hanyoyin hana shugaba Bola Ahmed Tinubu lashe zabe a 2023
  • Ƙungiyar Arewa Youth Assembly ta yi zargin cewa wasu gwamnonin sun shirya tayar da rikici a jam'iyyar APC domin hana Tinubu tazarce
  • Matasan sun bukaci gwamnonin da ake zargi da su fito su ba shugaban kasa, jam'iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki hakuri kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ƙungiyar Arewa Youth Assembly ta nuna rashin jin daɗinta kan zargin cewa wasu gwamnoni na shirya yadda za su haddasa rikici a cikin jam’iyyar APC.

Ta yi zargin cewa an shirya tayar da rikicin ne domin hana Mai girma shugaba Bola Ahmed Tinubu sake lashe zaɓe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

'Yadda 'yan Arewa za su zabi Tinubu a 2027,' Uba Sani ya fito da bayanai

Shugaba Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a ofis. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Rikicin da za a kulla a jam'iyyar APC

Daily Trust ta wallafa cewa kakakin ƙungiyar, Mohammed Sanni ya yi zargin cewa wasu ’yan siyasa na ƙoƙarin haddasa rarrabuwar kai a cikin ƙungiyar gwamnonin APC domin jefa rikicin cikin gida.

Ƙungiyar ta zargi wasu gwamnoni biyu daga Kudancin ƙasar da jagorantar yunƙurin cire shugaban ƙungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma.

A cewar ƙungiyar, wannan mataki ya yi kama da abubuwan da suka faru kafin babban zaɓen shekarar 2015, wanda suka ce ya taimaka wajen kayar da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.

Arewa Youth Assembly ta yi zargin cewa ana kai wa Uzodimma hari ne saboda yadda ake kallonsa a matsayin mai biyayya ga shugaba Tinubu da kuma rawar da yake takawa wajen tara goyon baya domin wa’adi na biyu na shugaban ƙasar.

“Bayanan sirri da muke da su sun nuna cewa suna son haddasa rikici a cikin ƙungiyar gwamnonin APC a matsayin matakin farko na rusa jam’iyyar daga ciki,”

Kara karanta wannan

"Da hannun Tinubu": ADC ta yi fallasa kan 'dalilin' farfado da jam'iyyar NDC

In ji ƙungiyar.

Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo
Lokacin da gwamna Hope Udozimma ya saye fom din sanata. Hoto: Imo State Government
Source: Facebook

Karfin gwamnoni a jam'iyyar APC

Rahoton Trust Radio ya nuna cewa kungiyar ta ce gwamnonin APC su ne “ƙarfin jam’iyyar,” kuma suna da muhimmanci wajen tabbatar da sake zaɓen Tinubu a 2027.

Sai dai ƙungiyar ta yaba wa gwamnoni — musamman na Arewa — saboda tsayawa tare da Uzodimma da kuma goyon bayan tsarin karɓa-karɓa wanda zai bai wa yankin Kudu damar kammala wa’adinsa a mulki zuwa shekarar 2031.

Ƙungiyar ta kuma bai wa gwamnonin da abin ya shafa wa’adin awa 48 su ba shugaba Tinubu da APC da kuma ƙungiyar gwamnonin APC haƙuri kan abin da ta bayyana a matsayin mummunan yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba.

Gwamna Uzodimma zai nemi sanata

A wani labarin, kun ji cewa gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo ya saye fom din takarar sanata a zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Shugaban gwamnonin APC, Uzodimma ya bayyana cewa hakan na cikin shirye-shiryen da ya ke domin ganin ya cigaba da kawo cigaba a jiharsa.

Sayen fom din Uzodimma ya ja hankalin jama'a ne lura da cewa har zuwa zaben 2027 wa'adinsa na gwamna ba zai kare ba, sai bayan 2028.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng