Saudiyya Ta Shiga tsaka Mai Wuya, Iran Ta Matsa Mata Lamba Ta Fannoni 3 a Yaki da Amurka

Saudiyya Ta Shiga tsaka Mai Wuya, Iran Ta Matsa Mata Lamba Ta Fannoni 3 a Yaki da Amurka

  • Saudiyya ta fara kai farmaki tare da Amurka kan ƙawayen Iran a Iraki bayan zargin su da kai hare-haren jiragen sama marasa matuki
  • Yarima Mohammed bin Salman na kokarin kare shirin Vision 2030 saboda rikicin na barazana ga zuba jari da muhimman cibiyoyin tattalin arziki
  • Hare-haren da aka kai kan cibiyoyin man fetur na Saudiyya sun nuna irin barazanar da jiragen sama marasa matuki da makamai masu linzami ke haifarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Saudiyya - Kasar Saudiyya na fuskantar babban ƙalubale yayin da rikicin da ya biyo bayan yaƙin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu ke ci gaba da faɗaɗa.

Duk da ƙoƙarin da Riyadh ta yi na kauce wa shiga rikicin kai tsaye, hare-haren da ta ce ana kai mata daga sassa daban-daban sun tilasta mata ɗaukar matakin mayar da martani.

Kara karanta wannan

Tsohon IGP ya fallasa gwamnati, ya fadi abin da ya jawo lalacewar tsaron Najeriya

Saudiyya ta shiga tsaka mai wuya a yaki da Iran
Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman. Hoto: @HaramainInfo
Source: Twitter

A wannan mako, rundunar Saudiyya tare da haɗin gwiwar Amurka sun kai hare-hare kan ƙungiyoyin mayaƙan da Iran ke marawa baya a Iraq, bayan zargin cewa suna ƙaddamar da hare-haren jiragen yaƙi marasa matuƙi kan masarautar in ji rahoton BBC.

Rikicin ya raba yankin zuwa bangarori 2

A cewar rahoton, rikicin ya haɗa manyan bangarori biyu. A gefe guda akwai Iran da rundunar Islamic Revolutionary Guards Corps (IRGC), tare da ƙawayenta da suka haɗa da Houthis na Yemen, Popular Mobilisation Forces (PMF) na Iraq da kuma Hezbollah ta Lebanon.

A ɗaya bangaren kuma akwai Amurka da rundunar Centcom, tare da wasu ƙasashen Larabawa na yankin Gulf da Jordan. Rahoton ya ce Isra'ila, duk da kasancewarta ƙawar Amurka, ba ta shiga wannan yaƙin kai tsaye a halin yanzu.

An zargi ƙawayen Iran da kai hare-hare

Rahoton ya ce Iran ta fi mayar da hankali wajen kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙi kan Jordan, Kuwait da Bahrain, tare da kai hari ga jiragen ruwa da ke bi ta mashigin Hormuz ba tare da bin sabbin ƙa'idojin Tehran ba.

Kara karanta wannan

An daura auren gata ga mutum 300 a Kebbi, gwamnati za ta cigaba da shirin

Haka kuma, ana zargin mayaƙan PMF a Iraq da Houthis a Yemen da ƙara faɗaɗa rikicin, lamarin da ke nuna cewa yankin na iya shiga cikin yaƙi mafi girma idan ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran ba.

Dalilin da Saudiyya ke son kauce wa yaƙi

Rahoton ya bayyana cewa Yarima Mai jiran gado Mohammed bin Salman na ci gaba da aiwatar da shirin "Vision 2030", wanda ke da nufin rage dogaro da kuɗin man fetur tare da bunƙasa masana'antu da jawo hannun jarin ƙasashen waje.

Sai dai wannan buri na iya fuskantar barazana idan hare-haren jiragen yaƙi marasa matuƙi daga Yemen ko makamai masu linzami daga Iran suka ci gaba da kai wa cibiyoyin tattalin arzikin ƙasar hari.

Harin 2019 ya nuna raunin tsaron Saudiyya

Rahoton ya tuna cewa a watan Satumbar 2019, wasu mayaƙan da ake dangantawa da Iran sun kai hari kan manyan cibiyoyin man fetur na Abqaiq da Khurais, lamarin da ya dakatar da kusan rabin fitar da man fetur na Saudi Arabia na wasu kwanaki.

Ko da yake a lokacin an yi zargin Houthis ne suka kai harin, binciken da aka gudanar ya nuna alamun cewa hare-haren sun fito ne daga arewa, abin da ya ƙara nuna yadda manyan cibiyoyin ƙasar ke da rauni.

Kara karanta wannan

An fitar da hotunan yaran da ake ba horo kan jirage marasa matuka

Rahoton ya ƙara da cewa hotunan tauraron ɗan adam da aka ɗauka a ranar Litinin sun nuna cewa cibiyar man fetur ta Abqaiq ta sake fuskantar hari daga jiragen yaƙi marasa matuƙi da ake zargin mayaƙan da Iran ke marawa baya a Iraq ne suka harba.

Rahoto ya nuna cewa Saudiyya tana son kaucewa yakin Iran da Amurka.
Ganawar Shugaba Donald Trump tare da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman. Hoto: @HRHMBNSALMAAN
Source: Twitter

Saudiyya na fuskantar zaɓi mai wahala

Yanzu haka, babban ƙalubalen da ke gaban Saudi Arabia shi ne ko ta ci gaba da mayar da martani domin hana ƙarin hare-hare, ko kuma ta nemi rage zafin rikicin ta hanyar sasanta da wasu daga cikin masu tayar da ƙayar baya.

Masana na ganin matakin da Riyadh za ta ɗauka a makonni masu zuwa zai iya tasiri sosai kan makomar tsaron yankin Gabas ta Tsakiya da kuma kasuwar man fetur ta duniya.

Saudiyya ta kori jakadun Iran

A wani labari, mun ruwaito cewa, kasar Saudiyya ta sallami wasu daga cikin jami’an diflomasiyyar Iran biyar tare da ba su awa 24 su fice daga kasar.

Matakin ya biyo bayan hare-haren jiragen sama marasa matuki da makamai da ake zargin Iran na kai wa cibiyoyin mai da fararen hula.

Rikicin Amurka, Isra'ila da Iran ya kara dagula yankin tare da tasiri kan kasuwar makamashi ta duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com