Shugaba Tinubu Ya Amince da Sabon Aikin N46bn a Kano

Shugaba Tinubu Ya Amince da Sabon Aikin N46bn a Kano

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 46 domin sake shimfiɗa da kuma gina titin saukar jiragen sama na biyu a filin jirgin saman Kano
  • Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya ce aikin zai ƙara inganta ayyukan filin jirgin tare da ɗaga martabarsa a duniya
  • Gwamnatin tarayya ta kuma fara aikin inganta tashar aikin Hajji a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano da ke birnin Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 46 domin gyara tashar jirgin sama ta Malam Aminu Kano (MAKIA).

Shugaba Tinubu ya amince da kudaden ne domin sake shimfiɗa da kuma sake gina titin saukar jiragen sama na biyu a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano.

Kara karanta wannan

An daura auren gata ga mutum 300 a Kebbi, gwamnati za ta cigaba da shirin

Tinubu ya amince da gyara filin jirgin sama na Aminu Kano
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta ce Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da sabuwar tashar cikin gida ta Muhammadu Adamu Dankabo da aka gyara tare da inganta ta a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano ranar Talata, 28 ga watan Yulin 2026.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai da sadarwa, Tunde Moshood, ya fitar, ministan ya ce aikin na daga cikin manyan shirye-shiryen da gwamnatin Shugaba Tinubu ke aiwatarwa domin bunƙasa harkokin sufurin jiragen sama.

Keyamo ya bayyana muhimmancin filin jirgin Kano

Festus Keyamo ya ce gwamnatin tarayya ta ware filin jirgin saman Kano domin samun manyan ayyukan ingantawa saboda muhimmancinsa ga tattalin arziki da harkokin sufuri.

Ya kuma ce hakan ne ya sa Shugaba Tinubu ya naɗa tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin shugaban hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN).

Kara karanta wannan

'Yan APC sun yi wa Peter Obi rubdugu da ya tabo Bola Tinubu

“Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ware filin jirgin saman Kano domin manyan ayyukan ingantawa saboda muhimmancin wannan filin jirgin."
“Shugaban ƙasa ya amince da ware Naira biliyan 46 domin sake shimfiɗa da kuma sake gina titin saukar jiragen sama na biyu, domin filin jirgin saman Kano ya iya gogayya da sauran manyan filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa.”

- Festus Keyamo

Za a gyara filin jirgin sama na Kano
Mai girma Bola Ahmed Tinubu zaune a ofis Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Gwamnati ta fara inganta tashar Hajji

Ministan ya sake jaddada kudirin gwamnatin tarayya na sauya fasalin harkokin sufurin jiragen sama a ƙarƙashin ajandar Renewed Hope ta Shugaba Tinubu.

Ya bayyana cewa Kano na da muhimmanci sosai ga tattalin arzikin Najeriya, yana mai cewa birnin shi ne cibiyar kasuwancin Arewacin Najeriya, jaridar Leadership ta kawo labarin.

“Filin jirgin saman Mallam Aminu Kano shi ne zuciyar kasuwancin Arewacin Najeriya. Saboda haka muka ware Kano domin samun manyan ayyukan ingantawa.”

- Festus Keyamo

Tinubu ya yabawa Umahi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya taya Ministan Ayyuka, David Umahi, murnar cika shekara 63 da haihuwa a duniya.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta hango kura kurai a kalaman Obi, ta yi masa zazzafan martani

Shugaba Bola Tinubu ya yaba da jajircewarsa wajen aiwatar da ayyukan more rayuwa masu ɗorewa a faɗin tarayyar Najeriya.

Mai girma Bola Tinubu ya yabawa Umahi kan ƙwazonsa, sadaukar da kai ga aiki, da kuma kishin ƙasa da yake nunawa wajen gudanar da ayyukansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng