'Na Shirya a Yi Tonon Silili': Pantami Ya Bugi Kirji kan Abubuwan Alheri da Ya Yi

'Na Shirya a Yi Tonon Silili': Pantami Ya Bugi Kirji kan Abubuwan Alheri da Ya Yi

  • Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana dalilinsa na shiga takarar gwamnan Gombe a 2027, yana mai korafi kan lalacewar lamura
  • Pantami ya bayyana cewa babu wata al'umma da ta gyaru da kanta, yana mai cewa sai mutane sun tashi tsaye domin neman sauyi
  • Pantami ya bukaci a shirya muhawara tsakanin dukkan 'yan takara, tare da binciken ayyukansu da ba da damar tonon silili kafin zaben gwamna na 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana shirin da ya yi game da zaben gwamna na shekarar 2027 da ke tafe.

Malam Pantami na daga cikin masu neman takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar PDP wanda za a yi a 2027.

Pantami ya bukaci shirya muhawara a Gombe
Dan takarar gwamnan Gombe a APC, Jamilu Isiyaku Gwamna da takwaransa na PDP, Isa Ali Pantami. Hoto: Ismaila Uba Misilli, Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Malam Pantami ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da Premier Radio ta wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa: 'Tinubu ya fitar da mara 'da kunya, ya kamata a saka masa a 2027'

Musabbabin shigan Pantami siyasa a Najeriya

A cikin bidiyon, Pantami ya ce ko kadan bai yi niyyar shiga siyasa ba sai domin kawo gyara a ƙasa.

Pantami ya ce idan da komai na tafiya daidai da babu abin da zai saka shi tsunduma harkar siyasa.

Ya ce:

"Allah ya sani idan da komai na tafiya daidai a jihar Gombe da Najeriya, babu abin da zai shigo da mu harkar siyasa, amma lalacewar lamura, sai ya zama ba tunani ne na mai cikakken hankali cewa wai idan lamura suka lalace kowa sai ya koma gefe ya kalla.
"Tun farkon duniya zuwa yau, babu wata alumma da ta lalace da aka koma aka zauna Allah da kansa ya zo ya gyara.
"Sai dai wasu a ciki su yi yunkurin gyara sai Allah ya taimake su a gyara, ba a taɓa wani lalaceccen tsari da ya gyara kansa ba, wannan ya sa muka hakura da jin dadinmu da walwala da zama da iyalai muka ce ba za mu bari zamani ya lalace ba."

Kara karanta wannan

An taso Tinubu a gaba game da lafiyarsa kan sake neman takara a 2027

Isa Ali Pantami ya bugi kirji kan abubuwan alheri da ya yi
Dan takarar gwamnan Gombe karkashin PDP, Isa Ali Pantami. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Twitter

Bukatar Pantami ga sauran yan takara

Malam Isa Pantami ya bukaci a shirya muhawara ga dukkan yan takara domin kowa ya bayyana manufofinsa kan zaben.

Ya bukaci ware awanni shida tare da samar da dukan gogaggun yan jarida domin tabbatar da cewa an yi muhawarar yadda ya dace.

"Kowa ya kawo abubuwan da ya yi a baya, sannan a bincike abin da na ce nima na binciki wanda ya kawo domin a yi keke da keke."
"Sannan a ba da lokacin tonon silili, mai amana ake kara ba amana, maci amana idan aka kara ba shi amana an yi wa Allah laifi."

- Isa Ali Pantami

Tafiyar Pantami ta sake samun karfi

An ji cewa tsohon mai neman takarar gwamnan Gombe a karkashin PDP, Mohammed Manu Malala, ya goyi bayan Prof. Isa Ali Ibrahim Pantami.

Mohammed Manu Malala ya ce ya ajiye burinsa na neman takarar gwamna ne domin hadin kan jam’iyya da ci gaban Gombe.

Ya kuma musanta rahotannin cewa ya kai kara kan zaben fitar da gwani na dan takarar PDP na gwamna a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.