Shugaban Sojojin Najeriya
Rundunar sojin Najeriya ta karrama jami’ai da sojojin Operation Lafiya Dole su 37 sakamakon hakazakarsu wajen yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar.
Sai kuma gashi a ranar Alhamis shugaba Buhari ya kira wani taro na gagga wa da shugabannin rundunonin tsaro na kasa a fadarsa, lamarin da yasa wasu suke zargin cewa taron ba zai rasa nasaba da kiran neman Buhari ya yi murabus ba.
Wata Hadimar Shugaban kasa ta dirkawa Sanatan da ya nemi Muhammadu Buhari ya yi murabus zagi. Hadimar ta ce Sanatan ya fara dauko dutse ya jefi Buhari, su na jiransa.
Shugaban kungiyar CHRSJ, Adeniyi Sulaiman ya sake hurowa Buhari wuta ya tsige Shugabannin Sojojin Najeriya saboda matsalar harkar tsaro.
IPhone 11 ta sa wani Matashi ya aika ‘Danuwansa lahira a Anambra. Yanzu ‘Yan Sanda sun kama wannan Matashi wanda ya hallaka ‘Danuwansa na ciki.
Shugaban Majalisar Dattawa watau Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya yarda akwai matsalar tsaro. Ahmad Lawan da Osinbajo sun koka da halin da ake ciki a Najeriya.
A makon jiya mu ka ji cewa NSCDC ta bukaci ayi bincike a kan kisan Ndubuisi Emenike bayan Jami’in tsaron ta ya kashe ‘Dan siyasa a Imo.
Jam’iyyar PDP ta na so ‘Yan Majalisa su taso mata keyar Buhari kwanan nan. PDP ta ce ‘Yan Majalisa su gayyato Buhari ya yi bayani kan kashe-kashen da ake yi a Najeriya.
A jiya Mahaifin Leah Sharibu ya yi magana game da rade-radin haihuwar ‘Diyarsa. Sharibu cikin fushi, yake cewa ban yarda ‘Diyata ta auri ‘Dan Boko Haram har sun haihu ba.
Shugaban Sojojin Najeriya
Samu kari