Hadimin Buhari Ya Fito da Hakikanin Abin da Ya Faru a Zaben Gwamnan Osun
- Babafemi Ojudu ya yi bayanin abin da ya sa jam’iyyar Accord ta ba jama’a mamaki a zaben gwamnan Osun
- Tsohon ‘dan jaridan da ya shiga siyasa daga baya ya ce mutanen jihar Osun na dabam ne a siyasa tun ba yau ba
- Sanata Ojudu ya kuma bada labarin yadda aka hana sakataren ADC na kasa, Rauf Aregbesola sakat ta ko ina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Babafemi Ojudu ya cigaba da yin magana game da zaben gwamna da aka yi a jihar Osun a karshen makon da ya gabata.
Bayan hukumar INEC ta fadi wanda ya yi nasara a takarar gwamnan Osun, ya yi magana kan yadda aka rabu da siyasar jam’iyya.

Source: Twitter
Sharhi kan zaben da aka yi a Osun
A shafinsa na Facebook, babban ‘dan siyasar ya ce ana ta yi masa tambayoyi game da muguwar rawar da Rauf Aregbesola ya taka.

Kara karanta wannan
Bayan shan kashi a Osun, shugaban matasan APC ya ba jam'iyyar mafita kan zaben 2027
Ya bada amsa a rubutun da ya yi mai kalmomi kimanin 700 da ya yi wa take da 'Abin da ya sa masu zabe a Osun suka kyale siyasar jam’iyya.'
Da farko ya fara tuna wa mutane cewa Rauf Aregbesola bai cikin ‘yan takara, sai dai an cusa shi cikin yakin neman gwamna da aka yi.
Baba Hafusa: Yadda aka kashe kasuwar Aregbesola
Rubutun ya ce an yi kokari wajen ganin an yi maganin tsohon ministan harkokin cikin gidan ta yadda ADC ba ta iya yin tasiri a Osun ba.
Ya ce:
"An yi ta kai wa ‘dan takaransa hari ta kowane lungu. Jam’iyyar Accord ta yi ta maganar biyan ma’aikata rabin albashi da Aregebesola ya yi, yayin da aka yi watsi da nasarorinsa a fannin gina mutane da abubuwan more rayuwa.
"A matakin kasa, da Aregbesola ya yi nasara a Osun, da ya aika sako ba a iyaka kasar Yarbawa kawai ba, duk fadin Najeriya."
"A wannan takarar, Aregbesola ne makiyin da aka ga bukatar a fara kawar da shi.
Sai dai tsohon hadimin shugaban kasar ya nuna shakkunsa kan abin da zai iya biyo baya sakamakon nasarar jam’iyyar adawa kan APC.
Rikicin cikin gidan da yake ADC
A rubutun ne Sanata Ojudu ya fito da rikicin cikin gidan ADC, ya ce ko a reshen Osun akwai baraka tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar adawar.
Dayan bangaren da ba su tare da su David Mark sun yaki tsohon gwamnan da ‘yan tafiyarsa ta Omoluabi har Ademola Adeleke ya yi nasara.
Ojudu ya ce baya ga wayewar mutanen Osun, an shiga tsakanin Aregbe da Atiku, wannan ya sa ‘dan takaran ADC bai kai ko ina ba.
"‘Yan wannan tsagi suna da fada wajen Atiku da matarsa Titi kuma sun yi nasarar rage karfin amannar da suka yi da shi (Aregbesola)
Na fahimci cewa mutanen Aregbesola ba su samu akalla wata gudumuwar kirki daga Atiku wanda yanzu shi ne ‘dan takaran shugaban kasa ba."
- Babafemi Ojudu
Wayewar mutanen Osun ta yi tasiri a zabe
Wasu ‘yan ADC sun sha alwashin kawo karshen siyasar Gboyega Oyetola da mutanensa, don haka suka rabu da jam’iyyarsu a zaben.
Ya ce Osun wayayyiyar jiha ce da ta tara garuruwa masu tarihi kamar Ilesa, Ede, Iwo Ejigbo, Ile-Ife, Ikire, Ikirun, Ila-Orangun da Oke-Ila.
Ko a zaben 2011 an ga halin ‘yan Osun, wadanda suka zabi Nuhu Ribadu a lokacin da Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari ke tashe.
Wadanda Adeleke ya tika da kasa
Kun samu rahoto dauke da jerin fitattun ‘yan APC a Osun da Ademola Adeleke ya kunyata a zaben gwamna da aka shirya ranar Asabar.
Hadimin Muhammadu Buhari ya ce cikin wadanda aka dankara da kasa har da sanatan da ya ce a ‘kashe’ ‘yan jam’iyyar Accord a Osun.
Nasarar gwamnan tana nufin an yi wa mutane irin su Gboyega Oyetola da sanatan ganashin Osun lahani.
Asali: Legit.ng

