Masunta su na biyan ‘Yan Boko Haram harajin kamun kifi a tafkin Chad

Masunta su na biyan ‘Yan Boko Haram harajin kamun kifi a tafkin Chad

Daga cikin sana’o’in da rikicin Boko Haram ya kawowa cikas a yankin tafkin Chadi akwai harkar su na kamun kifi da noman barkono. Da wadannan sana’a da-dama su ka dogara a baya.

A shekarar 2015, jaridar HumAngle ta ce labarin ya fara sauyawa a yankin na tafkin Chadi da ke kasar Borno. An samu raguwar kudin shigan da Najeriya ta ke samu wajen fita da kifi waje.

‘Yan ta’addan Boko Haram wanda su ka rikida su ka zama kungiyar ISWAP sun yi amfani da wannan dama na kasuwanci, su ka shiga gayyatar mutanen da ke IDP su koma bakin sana’arsu.

Ganin irin halin da wadannan mutane da ke sansanin gudun hijira su ka tsinci kansu, dole ta sa wasu su ka amsa goron gayyatar ‘yan ta’addar, su ka dawo tafkin Chadi domin cin kasuwa.

Yanzu kasuwar kifi ta budewa wadannan Bayin Allah da ke sana’a kan iyakar Najeriya da Chad. Wani daga cikin masu su ya nuna cewa su na biyan ‘yan ta’addan haraji na sana’ar da su ke yi.

KU KARANTA: Shugaban Boko Haram ya na neman mika kansa gaban Jami'an tsaro

Masunta su na biyan ‘Yan Boko Haram harajin kami kifi a tafkin Chad
Shugaban hafsun sojin kasan Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai
Asali: Twitter

Adamu Baga ya yi magana da HumAngle inda ya ce su kan biya kudin haraji a kan kowane gasasshen kifi da buhun barkono da su ka samu. Adamu ya ce shekaru uku kenan ana wannan.

Wannan mutumi ya shaidawa ‘yan jarida cewa su kan biya N400, 000 zuwa N500, 000 a shekaru ukun nan da su ka wuce. A cewarsa, ya na cikin manyan masu samun kudi da wannan sana’a.

Rahoton ya ce bayan haraji da ake biyan ‘yan ta’addan Boko Haram, kungiyar ta kan samu kudi ta hanyar bada tsaro ga manoman domin su iya saida kayansu tsaf a kasuwannin da ke yankin.

Bugu da kari ‘yan ta’addan su kan yi sana’ar su domin su samu kudi ta cinikin kifi. Wani mutumi ya shaidawa jaridar cewa ana raba kudin da ake samu ne tsakanin sojoji da ‘yan ta’adda.

Wani masunci da ke garin Bama ya ce su kan biya N15, 000 duk bayan mako biyu a matsayin haraji. Haka zalika masunta su kan saida kwalin kifi kan farashi mai sauki ga ‘yan ta’addan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel