Dalilai 15 da Suka Sa APC Ta Sha Kasa a Zaben Jihar Osun

Dalilai 15 da Suka Sa APC Ta Sha Kasa a Zaben Jihar Osun

  • Tsohon Sanata Ojudu Babafemi ya bayyana dalilai 15 da yake ganin suka yi sanadiyyar rashin nasarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan Jihar Osun
  • Ojudu ya ambaci yunwa da matsin tattalin arziki, daskarar da asusun gwamnatin jihar da kuma kalaman Gwamnan Edo a matsayin wasu daga cikin dalilan
  • Jigon na APC ya kuma ambaci rawa da Adeleke ke yi, tasirin mawaki Davido a matsayin wasu daga cikin abubuwan da suka taimaka wa Accord wajen samun nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Osun – Tsohon Sanata Ojudu Babafemi ya bayyana jerin dalilai 15 da ya ce sun taimaka wajen kayar da jam’iyyar APC a zaben gwamnan Jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar.

Ojudu, wanda ya wakilci Ekiti ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ya fadi jerin abubuwan ne Lahadi, 17 ga Agusta 2026.

Kara karanta wannan

Dalilai 5 da suka sa Adeleke ya tumurmusa APC a zaben Osun

Gwamna Ademola Adeleke
Gwamna Ademol Adeleke da ya yi tazarce a Osun. Hoto: Osun State Government
Source: Facebook

A wani sako da ya wallafa a Facebook, Ojudu ya fara da ambaton yunwa da tsadar rayuwa da ake fama da su a kasar a matsayin daya daga cikin manyan abubuwan da suka sa masu zabe suka juya baya ga jam’iyyar APC.

Abubuwa 15 da Ojudu ya ambata

1. Yunwa a Najeriya

Legit ta rahoto Ojudu ya ce duk wanda ya ke da alhakin matsalar yunwa da ake fama da ita a kasar ya taimaka wajen kayar da APC a zaben

2. Kalaman Gwamnan Edo

Ya ce kalaman da Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya yi kan Adeleke sun fusata mutane tare da kara wa gwamnan Osun goyon baya.

3. Daskarar da asusun Osun

Ojudu ya zargi wanda ya ba da umarnin daskarar da asusun gwamnatin Jihar Osun da taimakawa wajen kara wa Adeleke goyon bayan jama’a.

4. Maganar Sanata Fadahunsi

Legit ta rahoto cewa ya ambaci Sanata Francis Fadahunsi saboda kalaman da aka danganta da shi na cewa ya kamata a kashe ‘yan jam’iyyar Accord.

Kara karanta wannan

Yadda motoci suka nutse, komai ya tsaya cak bayan ambaliya a Abuja

5. Maganar Wole Oke

Ojudu ya ce Wole Oke ya rika yawo yana alfahari da sunan Shugaba Bola Tinubu da karfin da yake da shi, abin da ya ce bai taimaka wa APC ba.

6. Ero Arike

Tsohon Sanatan ya kuma ambaci Ero Arike saboda kalaman da ya bayyana a matsayin yawan surutu, zagi da la’ana.

7. Maganar Gboyega Oyetola

Ojudu ya zargi tsohon Gwamnan Osun, Gboyega Oyetola, da tilasta wa jam’iyyar wani dan takara da bai yi farin jini sosai ba tare da hana mambobin APC damar zabar dan takarar da suke so.

8. Gwamnoni da shugabannin APC

Ya ce zuwan wasu gwamnonin jihohi da shugabannin jam’iyyar APC jihar Osun kafin zaben ya kasance kamar sun zo ne domin kwace jihar, lamarin da ya iya fusata masu zabe.

Gwamna Ademola Adeleke
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke. Hoto: Osun State Government
Source: Facebook

9. Rawar Gwamna Adeleke

Tsohon sanatan ya ce yadda Adeleke ke rawa ba tare da gajiyawa ba ya taimaka wajen kara kusantar da shi da jama’a.

Kara karanta wannan

Ana korafi a kan zargin lakadawa Musa Mai Sana'a duka kan tallan Tinubu a Katsina

10. Tasirin Davido

Ojudu ya kuma ambaci mawaki Davido, da abin da ya kira karfin da yake da shi wajen jawo dimbin jama’a a yakin neman zaben Adeleke.

11. Kaddamar da ayyukan gwamnati

Ya ce shawarar da aka bai wa Adeleke na kaddamar da ayyuka da dama gab da zabe ta taimaka masa wajen samun karin gani da kuma halaccin siyasa, musamman kasancewar sarakunan gargajiya suna halartar wasu daga cikin tarukan.

12. Al’ummar Osun

Ojudu ya yabawa al’ummar Osun saboda abin da ya bayyana a matsayin jarumta wajen tunkarar ‘yan daba da aka zargi an tura su domin kwace akwatunan zabe.

Ya ce wasu daga cikin masu zaben sun kwace bindigogi da gatari daga hannun wasu daga cikin ‘yan daban.

13. Wakokin yakin neman zabe

Ya kuma ambaci fasahar al’ummar Osun wajen kirkirar wakokin yakin neman zabe masu dauke da kalamai masu kaifi da suka taimaka wajen isar da sakon siyasa.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Aikin Davido da abubuwa 5 da suka taimaki Adeleke ya sake doke APC

14. Masu tsara yakin Adeleke

Ojudu ya yabawa masu tsara yakin neman zaben Adeleke, musamman wadanda suka shirya shi domin muhawarar ‘yan takara, inda ya ce ya zarce abin da mutane da dama suke tsammani.

15. Masu yada labaran Adeleke

A karshe, tsohon sanatan ya yabawa tawagar yada labarai ta Adeleke, yana mai cewa ta yi kyakkyawan aiki wajen tallata dan takararta da isar da sakonsa ga jama’a.

Davido ya caccaki Okpebholo

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya yi wa Adeleke ba’a kan yadda yake rawa a bainar jama’a yayin yakin neman zaben APC a Osun.

Okpebholo ya tambayi ko al’ummar Osun sun gaji da ganin gwamnan yana rawa kafin sanya hannu kan takardu ko halartar tarukan gwamnati.

Bayan nasarar Adeleke, mawakin Afrobeats, Davido, ya sake mayar da martani ga Gwamnan Edo a shafinsa na Instagram, inda ya gargade shi da ya shirya domin martanin da zai biyo bayan nasarar Adeleke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng