Borno: Buratai ya rabawa sojoji abinci yayin bikin ista a sansanin soji a Ngamdu
A wasu hotuna da jaridar SaharaReporters ta wallafa a shafinta na Tuwita, an babban hafsan rundunar sojojin kasa, Laftanat Janar Yusuf Tukur Buratai, a cikin dakarun soji ya na raba musu abinci yayin murnar bikin ista.
Bisa la'akari da yanayin fama da annobar cutar covid-19 da ake ciki, jaridar ta zargi Buratai da sabawa umarnin hukuma na nesanta da saka takunkumi domin rufe fuskarsu a matayin matakan dakile yaduwa cutar covid-19.
A makon jiya ne Buratai ya sanar da komawarsa yankin arewa maso gabas bayan rahotanni sun bayyana yadda sojojin kasar Chadi, a karkashin shugaban kasarsu, Idris Deby, suka ragargaji mayakan kungiyar Boko Haram.
Babban hafsan sojin, wanda ya yi murnar bikin ista ranar Litinin a sansanin sojoji da ke Ngamdu, ya bayar da tabbacin cewa nan bada dadewa ba za a murkushe sauran kungiyar Boko Haram duk da mayakan kungiyar sun dade su na barna.
Buratai, ya ci al washin cewa ba zai bar sauran rundunar sojoji da ke arewa maso gabas ba har sai ya ga bayan mayakan kungiyar Boko Haram a yankin.
"Ba zamu bar wannan yaki ya dade ba kamar yadda ta ke faruwa a wasu kasashe da suka shafe kusan shekaru 50 su na yaki ba. Ba zamu bari hakan ta faru ba a nan," a cewar Buratai.
DUBA WANNAN: Covid-19: 'Yan sanda sun kama manyan jami'an gwamnati da suka karya dokar hana taro
Janar Buratai ya bawa rundunar sojojin tabbacin cigaba da samun goyon bayan shugaban kasa, wanda ya bayyana cewa zai samar da duk abinda ake bukata domin a samu nasara a kan makiyan kasa.
Kazalika ya yi alkawarin cewa ba zai bar rundunar sojojin atisayen 'Lafiya Dole' ba har sai ya ga bayan mayakan kungiyar Boko Haram.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng