Boko Haram: Dakarun kasar Nijar sun hallaka ‘Yan ta’adda 76 a Sahel

Boko Haram: Dakarun kasar Nijar sun hallaka ‘Yan ta’adda 76 a Sahel

Jamhuriyar Nijar wanda ita ma ta na cikin masu fama da rikicin Boko Haram a yankin Sahel, ta yi wa wani namijin kokari inda ta hallaka ‘yan ta’ddan da-dama a shekaran jiya.

Rahotanni da mu ka samu daga AFP a ranar Larabar nan sun bayyana cewa Sojojin Nijar sun hallaka ‘yan ta’addan Boko Haram 75 a yankin na kudu maso gabashin Najeriya.

“An kashe ‘yan ta’adda 25 a ranar Litinin a kudancin garin Diffa, babban garin da ke kudu maso gabashin kasar Nijar, yayin da aka kashe wasu 50 a ranar a yankin tafkin Chadi.”

Ma’aikatar tsaron kasar wajen ta ce bayan sojojin Nijar sun ga bayan wasu ‘yan ta’ddan da ke cikin kasarsu, sun hallaka ‘yan Boko Haram kimanin 50 da ke fake a cikin Najeriya.

Jaridar ta bayyana cewa kawo yanzu ba a iya tabbatar da adadin wadanda ma’aikatar tsaron na kasar Nijar ta ce an kashe a wadannan hare-hare biyu da aka kai a cikin farkon nan.

KU KARANTA: An ji Abubakar Shekau ya na kuka a wani sabon faifai da aka fitar

“A ranar Litinin, sojoji daga cikin dakarun Nijar da ke yakin Boko Haram a Afrika su ka kai zafafan hare-hare a gabatar rafin Komadougou, su ka fafata da ‘yan Boko Haram.”

Ma’aikatar tsaron ta fitar da jawabi cewa dakarun sojojin makwabtan na Najeriya sun gwabza da mayakan Boko Haram ne a wani kauye da ke kusan kilomita 75 daga garin Diffa.

A wajen wannan arangama, an kashe sojoji biyu, an yi wa biyu mummunan rauni. Sojojin sun kuma iya karbe babura hudu, da makamai da harsashai daga hannun ‘yan ta’addan.

“A wannan rana an kashe kusan mayaka 50 a harin sama da luguden wutan da aka yi a Tombon-Fulani, wani tsibiri da ke cikin tafkin Chadi da ke arewa maso gabashin Najeriya.”

“An rusa mafakar ‘yan ta’addan a wannan hari.” Wannan yanki na Diffa ya na cikin inda ‘yan Boko Haram su ka addaba. Ko a kwanakin baya an kashe sojojin Najeriya a garin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng