Dalilai 5 da Suka Sa Adeleke Ya Tumurmusa APC a Zaben Osun

Dalilai 5 da Suka Sa Adeleke Ya Tumurmusa APC a Zaben Osun

  • Al’ummar Jihar Osun sun sake zabar Gwamna Ademola Adeleke domin ya jagoranci jihar a wa’adi na biyu bayan ya lashe zaben gwamna da aka gudanar ranar Asabar
  • Jami’in da ya jagoranci tattara sakamakon zaben, Joshua Olalekan Ogunwole, ya ayyana Adeleke a matsayin wanda ya yi nasara a safiyar Lahadi
  • Adeleke, wanda ya tsaya takara karkashin jam’iyyar Accord, ya samu kuri’u 511,067, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na APC, wanda ya samu kuri’u 444,815

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Osun – Gwamna Ademola Adeleke ya samu nasarar lashe zaben gwamnan Jihar Osun, inda ya doke ‘yan takara 14 da suka fafata da shi a zaben da aka gudanar ranar Asabar.

Nasarar Adeleke ta zo ne bayan ya bar jam’iyyar PDP, wadda ya yi takarar gwamna a karkashinta a shekarar 2022, zuwa jam’iyyar Accord, wadda ba ta da karfin siyasa irin na manyan jam’iyyun kasar.

Kara karanta wannan

Bayan shan kashi a Osun, shugaban matasan APC ya ba jam'iyyar mafita kan zaben 2027

Gwamna Ademola Adeleke
Gwamna Ademola Adeleke da ya lashe zabe karo na 2 a Osun. Hoto: Osun State Government
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun kawo muku wasu daga cikin muhimman dalilai biyar da suka taimaka wajen nasarar Adeleke.

1. Rufe da asusu Osun

Kwanaki kadan kafin zaben, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta rufe asusun gwamnatin Jihar Osun bisa zargin wasu harkokin kudi da ake bincike a kansu.

Hukumar ta ce ta fara binciken gwamnatin jihar tun watan Maris na 2026 kan yadda aka tafiyar da kudin Ecology Funds, Intervention Funds da kuma asusun FAAC da suka kai kimanin Naira biliyan 11.

Sai dai Shugaba Bola Tinubu ya shiga cikin lamarin tare da umartar EFCC da ta janye matakin da ta dauka kan asusun gwamnatin jihar.

Punch ta wallafa cewa matakin ya haifar da ce-ce-ku-ce kan lokacin da aka dauki matakin dakatar da asusun, lamarin da ya karawa gwamnan jihar farin jini wajen al'umma.

2. Biyan albashin ma’aikata

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Aikin Davido da abubuwa 5 da suka taimaki Adeleke ya sake doke APC

A lokacin mulkinsa na farko, Adeleke ya samu goyon bayan ma’aikatan gwamnati saboda yadda gwamnatinsa ta mayar da hankali kan biyan albashi da hakkokin ma’aikata da ‘yan fansho.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatinsa ta biya wani bangare mai yawa na basussukan albashi da fansho da ta gada daga gwamnatocin baya.

Adeleke ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta biya sama da Naira biliyan 80 daga cikin bashin fansho da ta gada, tare da biyan sama da kashi biyu bisa uku na bashin rabin albashin da ake bin ma’aikatan jihar.

Wannan ya sa ma’aikatan gwamnati, wadanda suke daga cikin manyan masu zabe a jihar, suka kasance cikin masu nuna goyon baya ga gwamnan.

3. Ayyukan da Adeleke ya yi

BBC ta wallafa cewa wani muhimmin abu da ya taimaka wa Adeleke shi ne ayyukan raya kasa da gwamnatinsa ta aiwatar a wa’adin farko.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gina kusan kilomita 350 na tituna, gina gadoji uku na sama, gyara tituna shida, tare da gyara sama da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 200.

Ya kuma ce an gyara makarantu 150 tare da samar da sabbin taraktoci 31 ga manoma.

Kara karanta wannan

Mutane 3 daga gidan Adeleke da suka shiga siyasa kuma suka shahara a tarihi

Adeleke ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta kara tallafawa manoma, bangaren ilimi da kiwon lafiya a jihar.

Ko da yake masu adawa da shi sun yi suka kan wasu daga cikin ayyukan, masu goyon bayan gwamnan sun yi amfani da su wajen nuna cewa ya cika wasu daga cikin alkawuran da ya dauka.

4. Kusancins Ademola da jama’a

Adeleke ya samu karbuwa musamman tsakanin matasa da ma’aikata saboda yadda yake hulda da jama’a.

An fi sanin gwamnan da nuna farin ciki da rawa a wajen tarukan jama’a, abin da wasu abokan hamayyarsa ke kallonsa a matsayin rashin kima, yayin da masu goyon bayansa ke kallonsa a matsayin wata hanya ta kusantar talakawa.

Shugaban Matasa na APC na kasa, Dayo Israel, ya ce rawa da Adeleke ke yi ba ta kasance masa matsala ba, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen sanya shi kusa da talakawa.

Adeleke kansa ya bayyana kafin zaben cewa yana da cikakken yakinin cewa ba zai fadi zaben ba, yana mai cewa ayyukan gwamnatinsa ne ya kamata jama’a su yi la’akari da su wajen yanke hukunci.

Kara karanta wannan

2027: NDC ta daura damara, za a yi wa gwamnan Kano abin da Accord ta yi a Osun

5. Rikicin siyasa kafin zabe

A watannin da suka gabaci zaben, jihar Osun ta fuskanci wasu abubuwan da suka shafi rikicin siyasa da tashin hankali.

Rahotanni sun nuna cewa an samu sama da abubuwa 73 da suka shafi tashin hankalin zabe a sassa daban-daban na jihar, yayin da rahotannin ‘yan sanda suka danganta mutuwar mutane 12 da rikicin siyasa a kananan hukumomi 14.

Adeleke ya bukaci Shugaba Tinubu da Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda da su kara tsaurara matakan tsaro domin kare jama’a da tabbatar da gudanar da zabe cikin lumana.

Ademola Adeleke da Davido
Mawaki Davido tare da Gwamna Ademola Adeleke. Hoto: Davido
Source: Instagram

Haka kuma, wata magana da aka danganta da Sanata Francis Fadahunsi, wadda aka yada a wani faifan bidiyo, ta haifar da ce-ce-ku-ce bayan an zarge shi da umartar magoya bayansa su kai hari ga ‘yan jam’iyyar Accord.

Daga bisani Fadahunsi ya musanta cewa kalaman nasa na nufin kisa, yana mai cewa bidiyon an kirkire shi ne da fasahar AI, kuma abin da yake nufi shi ne “a kashe su da kuri’u”.

Kara karanta wannan

Adeleke: Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da wanda ya lashe zaben gwamnan Osun

Tinubu ya taya Adeleke murna

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya taya Gwamna Ademola Adeleke murnar lashe zaben gwamnan Osun karo na biyu.

Tinubu ya kira Adeleke ta waya domin taya shi murna tare da bukatar ya hada kan al’ummar jihar bayan zaben da aka gudanar cikin tsananin fafatawa.

Shugaban ya bayyana nasarar Adeleke a matsayin wata alama da ke nuna cewa dimokuradiyya za ta ci gaba da samun karfi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng