Sanata Ndume ya jinjina ma Buratai bayan ya tare a fagen fama don yaki da Boko Haram

Sanata Ndume ya jinjina ma Buratai bayan ya tare a fagen fama don yaki da Boko Haram

Shugaban kwamitin Sojan kasa a majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume ya bayyana komawar babban hafsan Sojan kasa, Tukur Yusuf Buratai jahar Borno ya yi daidai.

Kamfanin dillancin labaru ta ruwaito Ndume ya bayyana haka ne a garin Yola, inda yace shirin da Buratai yayi na shiga a buga da shi a yakin da Sojoji suke yi da Boko Haram ya yi daidai.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Saudiyya ta baiwa mutane 1,676 marasa galihu tallafi a Kaduna da Kebbi

Ndume ya jinjina ma rundunar Soji sakamakon jajircewar da take nunawa wajen ganin ta murkushe kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, don haka ya nemi jama’a su basu hadin kai.

“Ina kira ga jama’an Borno, musamman wadanda suke zama a sanannun mafakar Boko Haram kamar su yankin tafkin Chadi, dajin Sambisa da tsaunukan Mandara, su taimaka ma Sojoji da bayanai.

Sanata Ndume ya jinjina ma Buratai bayan ya tare a fagen fama don yaki da Boko Haram

Sanata Ndume ya jinjina ma Buratai bayan ya tare a fagen fama don yaki da Boko Haram
Source: Facebook

“Ina kuma kira ga Sojoji dasu yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin cike gibin da za’a samu a yayin aikinsu saboda ta haka ne za’a samu kyakkyawar sakamakon da ake bukata.

“Akwai bukatar rundunar Soji ta hada hannu da matasan Civilian JTF da yan sakai don samun sahihan bayanan sirri game da zirga zirgan yan ta’addan.” Inji shi.

Daga karshe Sanata Ndume ya jinjina ma rawar da shugaban kasa Buhari yake takawa wajen shawo kan annobar Coronavirus, amma ya bayar da shawara game da rabon kayan tallafi.

“Kamata yayi a hada da gwamnoni, kungiyoyin addinai, kungiyoyin sa kai da hukumomin tsaro wajen rabon kayan tallafin da gwamnati take rabawa ma talakawa.” Inji shi.

A wani labari kuma, Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya taya jama’an garin Chibok alhinin cika shekaru 6 tun bayan da mayakan Boko Haram suka sace yan matan.

Wannan tasa gwamnan ya tura wata tawaga domin wakiltarsa wajen jajanta ma iyayen yan matan da yan uwansu, tare da taya su alhinin rashi, sa’annan kuma ya basu sako su kai musu.

Tawagar ta hada da kwamishinan ilimi, harkokin mata da kuma dan majalisa mai wakiltar Chibok a majalisar dokokin jahar, kuma sun isar da sakon gwamnan ya iyayen yan matan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel