Ba zan koma Abuja ba har sai an gama murkushe Boko Haram - Buratai

Ba zan koma Abuja ba har sai an gama murkushe Boko Haram - Buratai

Babban hafsan rundunar sojojin kasa, Laftanal Janar Yusuf Tukur Buratai, ya ci al washin cewa ba zai bar sauran rundunar sojoji da ke arewa maso gabas ba har sai ya ga bayan mayakan kungiyar Boko Haram a yankin.

A makon jiya ne Buratai ya sanar da komawarsa yankin arewa maso gabas bayan rahotanni sun bayyana yadda sojojin kasar Chadi, a karkashin shugaban kasarsu, Idris Deby, suka ragargaji mayakan kungiyar Boko Haram.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa Deby ya kwace wasu yankunan Najeriya daga hannun mayakan Boko Haram tare da jiran zuwan sojojin Najeria domin ya mika musu garuruwan.

Babban hafsan sojin, wanda ya yi murnar bikin ista ranar Litinin a sansanin sojoji da ke Ngamdu, ya bayar da tabbacin cewa nan bada dadewa ba za a murkushe sauran kungiyar Boko Haram duk da mayakan kungiyar sun dade su na barna.

Ba zan koma Abuja ba har sai an gama murkushe Boko Haram - Buratai
Janar Buratai
Asali: UGC

"Ba zamu bar wannan yaki ya dade ba kamar yadda ta ke faruwa a wasu kasashe da suka shafe kusan shekaru 50 su na yaki ba. Ba zamu bari hakan ta faru ba a nan," a cewar Buratai.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kashe 'yan bindiga 9, sun kubutar da mutane 18 a Zamfara

Janar Buratai ya bawa rundunar sojojin tabbacin cigaba da samun goyon bayan shugaban kasa, wanda ya bayyana cewa zai samar da duk abinda ake bukata domin a samu nasara a kan makiyan kasa.

Kazalika ya yi alkawarin cewa ba zai bar rundunar sojojin atisayen 'Lafiya Dole' ba har sai ya ga bayan mayakan kungiyar Boko Haram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel