Abin Tausayi: Hatsarin Jirgi Ya Rutsa da Manoma a Hanyar zuwa Gonakinsu a Najeriya
- Manoma biyar, maza huɗu da mace ɗaya, sun mutu bayan wani jirgin ruwa ya kife a Kogin Kudi da ke ƙaramar hukumar Katcha a Jihar Neja
- Rahotanni daga yankin sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Shaba-Woshi-Kpaya da ke gundumar Edotsu a ranar Asabar da rana
- Bayan faruwar lamarin, mutanen da suka iya ruwa sun shiga sun ciro gawarwakin manoman biyar kuma aka birne su a ranar Asaba din da ta wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Wani jirgin ruwa da ya dauko manoma ya nutse yayin da yake tsakiyar yafiya a jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa manoma biyar da suka kunshi maza huɗu da mace ɗaya, sun mutu bayan wani jirgin ruwa ya kife a Kogin Kudi da ke ƙaramar hukumar Katcha a Jihar Neja.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta ruwaito vewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Shaba-Woshi-Kpaya da ke gundumar Edotsu a yammacin ranar Asabar ta karshen makon da ya gabata.
Yadda hatsarin jirgin ruwan ya faru
Wani mazaunin yankin, Muhammadu Dan-Asabe, ya shaida wa manema labarai cewa mutanen suna kan hanyar zuwa gonakinsu ne lokacin da jirgin ruwan ya kife da su.
Daraktan yaɗa labarai da ayyuka na musamman na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dr Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce waɗanda abin ya rutsa da su suna tafiya ne daga ƙauyensu zuwa gonakinsu lokacin da jirgin ruwan ya kife, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsu a ruwa.
An birne wadanda suka mutu
Wannan al'amari dai ya girgiza jama'ar da ke zaune a yankin wannan kogi da ma al'ummar karamar hukumar Katcha ta jihar Neja.
An bayyana sunayen wadanda suka rasu a hatsarin jirgin da da Yahaya Abubakar, Usman Abubakar, Lami Hussaini, Baba Ahmadu da Salihu Aliyu.
Shugaban hukumar SEMA ya tabbatar da cewa an gano gawarwakin mutanen biyar kuma aka binne su a ranar Asabar din da ta wuce.

Source: Getty Images
Hatsarin jirgin ruwa a koguna
Hatsarin jiragen ruwa ya zama ruwan dare a wasu al’ummomin da ke zaune a bakin koguna, musamman lokacin noman rani ko damina, lokacin da mazauna yankunan ke dogaro da hanyoyin ruwa wajen zuwa gonakinsu.
Hukumomi na yawan dora laifin yawan hadurran da ake samu kan cika wa jiragen ruwa da kwale-kwale nauyin da ya wuce kima da kuma karya ka'idojin zirga-zirgar ruwa ta Najeriya.
Jirgin ruwa ya kife da manoma a Jigawa
A wani labarin, kun ji cewa mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da mutane 39 suka ɓace bayan wani kwale-kwale ɗauke da manoma da ma'aikata ya kife a Jigawa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Jigawa, SP Shi'isu Adam, ya ce rundunar ta samu rahoton hatsarin cikin gaggawa.
Ya bayyana cewa an samu nasarar gano gawar mutum ɗaya, yayin da ake ci gaba da aikin bincike da ceto domin gano sauran mutum 39 da har yanzu ba a san inda suke ba.
Asali: Legit.ng

