Sojoji sun kama manyan 'yan leken kungiyar Boko Harm 16, sun kashe mayaka fiye da 100

Sojoji sun kama manyan 'yan leken kungiyar Boko Harm 16, sun kashe mayaka fiye da 100

Kwalliya ta na cigaba da biyan kudin sabulu a atisayen KANTANA JIMLAN, wanda rundunar soji ta kirkira a karkashin atisayen LAFIYA DOLE domin karasa murkushe ragowar burbushin kungiyar Boko Haram.

Babban hafasan rundunar soji, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, ne ke jagirantar atisayen karasa murkushe kungiyar Boko Haram a sassan jihar Borno, musamman kusurwar yankin Timbuktu.

Matsin lambar da kungiyar Boko Haram ke fuskanta daga sojojin Najeriya ya rikita mayakan kungiyar tare da gwara kayuwan shugabanninsu.

A wata sanarwa da manjo janar John Enenche, shugaban sashen yada labarai na rundunar soji, ya fitar ranar Litinin, ya ce dumbin mayakan kungiyar Boko Haram sun rasa rayukansu yayin da su kai arba da sojoji.

"A wasu tagwayen hare - hare da rundunar soji ta kai a tsakanin ranar Juma'a da Asabar, ta samu nasarar kashe mayakan kungiyar kungiyar Boko Haram da ISWAP guda 78 tare da lalata wasu motocinsu na yaki a yankin Timbuktu.

"An kai hari kan mayakan ne ta sama da kasa bayan samun sahihan bayanai a kan wuraren da su ke buya a yankin.

"Wata rundunar sojojinmu da ke Buk a karamar hukumar Damboa ta samu nasarar kashe wasu mayakan kungiyar Boko Haram 56.

"Dakarun soji sun samu bayanan sirri a kan taron da mayakan kungiyar Boko Haram su ka kira a wani wuri da su ka yi kuskuren tunanin cewa ba za a iya kai mu su hari ta sama ba," a cewarsa.

Sojoji sun kama manyan 'yan leken kungiyar Boko Harm 16, sun kashe mayaka fiye da 100
Sojoji
Asali: Twitter

Jawabin ya ce 'yan tsirari ne daga cikin mayakan kungiyar su ka samu nasarar tserewa da munanan raunukan da ba lallai su tsira da ransu ba.

DUBA WANNAN: Ma su gudu su gudu: Bidiyon yadda jama'a su ka fece bayan wani mutum ya yanke jiki ya fadi a layin ATM

A cikin wata sanarwar da hedikwatar rundunar tsaron ta fitar, ta bayyana cewa manyan 'yan leken asirin kungiyar Boko Haram su 16 sun fada komar dakarun soji a cikin makonni biyu da su ka gabata.

"Kama manyan 'yan leken asirin Boko Haram ya kassara mayakan kungiyar wajen samun bayanai da kuma sadarwa a tsakaninsu," a cewar manjo janar Enenche.

Buratai, wanda ya shiga sati na biyar da komawa jihar Borno, ya taya dakarun sojin murnar kare martabar kasa da samun nasara a kan 'yan ta'adda.

Kazalika, ya bukaci su kara zage dantse tare da nuna rashin tausayi a kan makiyan kasa da yanzu haka ke neman hanyoyin tserewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel