Babban yaron Ganduje ya bar Kwankwaso da ya sauya sheka zuwa APC a Kano
- Abdulaziz Abdullahi Ganduje ya koma jam’iyyar APC wanda dama daga cikin ta ya fito ba da dadewa ba
- Shugabannin APC na mazabar Ganduje a karamar hhukumar Dawakin Tofa a Kano sun karbe shi ranar Lahadi
- A watan Mayu Abdulaziz ya rungumi NDC duk da mahaifinsa ya rike har shugabancin APC a matakin kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Zaman Abdulaziz Abdullahi Ganduje a jam’iyyar NDC ta kare a sakamakon wani sauya-sheka da ya sake yi a mazabarsa.
Kwanakin baya da madugun Kwankwasiyya ya fita daga ADC zuwa NDC, Abdulaziz Ganduje yana cikin mutanen da suka bi shi.

Source: Facebook
Abdulaziz Abdullahi Ganduje ya dawo APC
Watanni kadan da rasa tikitin tsayawa takarar Majalisar tarayya sai ga labarin canza gidan daga shafin Ibrahim Adam a Facebook.
A ranar Lahadi shugabannin APC na mazabar Ganduje a karamar hukumar Dawakin Tofa suka karbi yaron tsohon gwamnan jihar Kano.
Nan take kuma aka mika wa Abdulaziz Ganduje katin zama ‘dan jam’iyyar APC.
Jagorori da magoya bayan jam’iyyar APC musamman na karamar hukumar Dawakin Tofa sun shaida wannan canjin gida da aka yi ranar Lahadi.
Ina makomar Abdulaziz Ganduje a Kwankwasiyya?
Lokacin da ‘dan siyasar ya shiga NDC, ya so a tsaida shi ya wakilci mutanen Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado a Majalisar tarayya.
Kusan tun lokacin ya yi sanyi da tafiyar Kwankwasiyya wanda babban abokin hamayyar mahaifinsa yau a siyasa yake jagoranta a Najeriya.
Ko lokacin da ya ke karbar shaidar zama ‘dan APC, Abdulaziz yana sanye da jar hula, sai dai babu tabbacin zai cigaba da zama da ita.
Daily Trust ta ce shigowarsa APC bayan rufe saida takardar shiga takara ta tabbatar da bai da wuri a babban zabe mai zuwa na 2027.
Sai dai hakan za ta karfafi siyasar Ganduje a Kano tare da kashe rabuwar kafa tsakanin ‘ya ‘yan tsohon shugaban APC na kasar.
Abin da ake fada game da sauya-shekar
Hadimin gwamnan Kano da ya wallafa hotunan ya samu martani daga wadanda ba su rasa ta-cewa a dandalin sada zumuntan zamanin.
Ibrahim Adam ya rubuta:
"Abdulaziz Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga NDC kuma ya shiga APC a yau (Lahadi, 16 ga watan Agusta 2026) a garinsa na Ganduje."
Mahfuz M. Kamil da Kamal Garba LY godiya suka yi wa Allah, suna ganin wannan a matsayin alamar nasarar Abba Kabir Yusuf.
"Karin nasara ga APC"
- in ji Nazifi Yau Muhd.
Da ganin wannan kuwa babu abin da ya zo ran M. R. Sulaiman sai zaben Osun da aka yi inda jam’iyyar hamayya ta doke APC.
“Ya fahimta kenan”
- Aliyu Master Sudawa
Hamisu Bala Badawa ya rubuta:
“Da haka da haka in Allah ya yarda duk za su dawo bayan mai girma Gwamna”
Saminu Musa kuma yana ganin Kwankwaso bai kyauta wa yaron Gandujen ba.
Wani kuma ya tuno da wata waka mai cewa:
“An zo a ci banza, banza Ba ta samu ba sai a tashi a je gida”
Lokacin da Abdulaziz Ganduje ya je wajen Abba
An tuna lokacin da Abdul'aziz Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyara wajen gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a masaukin gwamnan da ke Abuja.
Hotunan ganawar da aka wallafa a kafafan sada zumunta sun tado ce-ce-ku-ce saboda adawar siyasa da ke tsakiyar bangaren Kwankwasiyya da Ganduje.
Mutane da dama sun bayyana mabanbanta ra'ayoyi, inda wasu ke ganin siyasa ce kawai yayin da wasu kuma ke kiran gwamnan ya ba shi mukami a Kano.
Asali: Legit.ng


