Ana Wata Ga Wata: Malamai Sama da 200 Sun Ajiye Aiki a Jami'ar Jihar Kaduna
- Kungiyar ASUU ta nuna damuwa kan yadda malaman jami’a sama da 200, ciki har da farfesoshi, suka ajiye aiki a jami’ar jihar Kaduna (KASU)
- Ƙungiyar ta bai wa gwamnatin Jihar Kaduna da mahukuntan jami’ar wa’adin makonni biyu su aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a bara
- ASUU ta yi barazanar fara yajin aikin gama-gari bayan karewar wannan wa'adi idan ba a cika buƙatunta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ta nuna damuwa kan sjiye aikin malamai sama da 200.
Shugaban ASUU-KASU, Dr Abubakar Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Litinin a Kaduna.

Source: Facebook
Malam KASU fiye da 200 sun ajiye aiki
Ya ce malaman, ciki har da farfesoshi, sun bar jami’ar ne saboda rashin kyawun yanayin aiki da kuma rashin fara aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya da ASUU suka cimma a 2025, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Abdullahi ya ce mafi yawan malaman da suka bar jami’ar sun samu guraben aiki a sababbin jami’o’i da aka kafa a cikin Jihar Kaduna da wajen jihar.
Ya danganta ficewar malaman da ƙarancin albashi da kuma tabarbarewar jin daɗin ma’aikatan jami’ar.
Ya ce ficewar ƙwararrun malaman jami’ar na iya yin mummunan tasiri kan koyarwa, bincike da ci gaban ilimi a KASU.
A cewarsa, maye gurbin ƙwararrun malaman da suka samu gogewa zai ɗauki shekaru tare da buƙatar kashe makudan kuɗaɗe.
ASUU ta ba gwamnatin Kaduna waa'di
Ƙungiyar ta kuma bai wa gwamnatin Jihar Kaduna da mahukuntan jami’ar wa’adin makonni biyu domin aiwatar da yarjejeniyar tare da shigar da ita cikin tsarin jami’ar.
ASUU ta yi gargadin cewa rashin ɗaukar mataki cikin wa’adin da ta bayar na iya haifar da fara cikakken yajin aiki mara iyaka a jami’ar.

Source: Twitter
A cewarsa, yarjejeniyar gwamnatin tarayya da ASUU ta shekarar 2025 ta fara aiki ne a watan Janairun 2026.
Ya ce yarjejeniyar ta tanadi inganta yanayin aikin malaman jami’o’in Najeriya. Sai dai shugaban ya ce har yanzu ba a fara aiwatar da yarjejeniyar a Jami’ar Jihar Kaduna ba.
Kungiyar ASUU ta nuna damuwa
Abdullahi ya ce ƙungiyar ta rubuta wasiƙu da dama zuwa ga mahukuntan jami’ar da majalisar gudanarwarta kan lamarin.
Ya nuna damuwa kan cewa sama da watanni takwas bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, har yanzu ba a fara aiwatar da ita ba.
Abdullahi ya ce jami’o’in gwamnatin tarayya da dama da wasu jami’o’in jihohi sun riga sun fara aiwatar da yarjejeniyar, kamar yadda Punch ta ruwaito.
ASUU za ta rufe jami'o'i 20 a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar ASUU ta ƙasa ta umarci jami’o’in jihohi kusan 20 su fara yajin aiki na sai baba-ta-gani cikin makonni biyu masu zuwa.
ASUU ta dauki wannan mataki ne saboda abin da ta bayyana a matsayin rashin tsari wajen aiwatar da sabuwar yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2025.
Asali: Legit.ng

