Abba Kyari: Tsohon Soja, Jami’in ‘Dan Sanda da Hadimin Shugaban kasa

Abba Kyari: Tsohon Soja, Jami’in ‘Dan Sanda da Hadimin Shugaban kasa

Mutane su kan samu kansu cikin rudani idan aka ambaci sunan Abba Kyari. Kyari ba bakon suna ba ne musamman a yankin Arewa maso gabas don haka sunan ya ke rikita wasu.

A Najeriya an yi akalla Abba Kyari uku wanda sunansu ya shahara. Rashin fahimtar hakan ne ya sa wasu kan cakuda mutanen kamar yadda aka gani bayan rasuwar Malam Abba Kyari.

A lokacin da Malam Abba Kyari ya fara kamuwa da COVID-19, wasu sun rika kiran DCP Abba Kyari su na yi masa jaje. Haka zalika wasu kan gaza banbance Janar Kyari da Malam Kyari.

1. Birgediya Janar Abba Kyari

Janar Abba Kyari shi ne kusan ainihin Abba Kyari da aka fara sani. Abba Kyari tsohon Soja ne wanda ya rike gwamnan Arewa a lokacin mulkin Gowon. A shekarar 2018 ne Kyari ya rasu ya na da shekaru 82. Wasu su kan alakanta wannan Bawan Allah da kuma Mallam Abba Kyari.

Abba Kyari: Tsohon Soja, Jami’in ‘Dan Sanda da Hadimin Shugaban kasa

Birgediya Janar Abba Kyari ya taba rike gwamnan tsohuwar Jihar Arewa
Source: Twitter

A lokacin da Janar Kyari ya ke gidan soja, ya taka rawar gani wajen hana kashe tarin Ibo a Arewa.

KU KARANTA: Mutanen Bauchi su na makokin mutuwar Malam Abba Kyari

2. DCP Abba Kyari

Akwai kuma wani babban jami’in ‘yan sanda wanda ya kai matakin mataimakin kwamishina mai suna Abba Kyari. DCP Abba Kyari ya yi suna wajen yin ram da gawurtattun barayi da masu garkuwa da mutane. Wannan Kyari ya fito ne daga Garin Gujiba da ke cikin jihar Yobe.

Abba Kyari: Tsohon Soja, Jami’in ‘Dan Sanda da Hadimin Shugaban kasa

Gwarzon Jami’in ‘Dan Sanda DCP Abba Kyari a bakin aiki
Source: Twitter

Kyari ya na cikin hazikan ‘yan sandan da ake da su, a halin yanzu ya zama dodon tsageru.

3. Malam Abba Kyari

Kusan Malam Abba Kyari ne mafi zama fitacce daga cikin masu wannan suna. Kyari ya rasu a ranar 17 ga watan Afrilu a shekara 67 bayan fama da ya yi da COVID-19. Malam Kyari mutumin jihar Borno ne kamar Janar Kyari, ya kasance shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya.

Abba Kyari: Tsohon Soja, Jami’in ‘Dan Sanda da Hadimin Shugaban kasa

Marigayi Abba Kyari lokacin ya na ofis a matsayin Hadimin Shugaban kasa Buhari
Source: Depositphotos

Ana zargin cewa Malam Kyari ya na cikin hadiman shugaban kasa masu karfi da aka taba yi.

A halin yanzu duka wadannan Bayin Allah sun rasu face DCP Abba Kyari. Baren cikin na su ya na da shekaru 45 ne yanzu a Duniya kuma ana hangen zai zama babba a gidan ‘yan sanda

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel