Bisa kuskure jami'anmu suka kashe Bala - Rundunar Sojin Najeriya

Bisa kuskure jami'anmu suka kashe Bala - Rundunar Sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya a karkashin atisayen OPSH a jihar Filato ta tabbatar da mutuwa wani matashi, Rinji Bala, mai shekaru 20, wanda ya ke aji uku a jami'ar Jos.

A ranar Talata ne dakarun rundunar OPSH suka harbi Bala, wanda aka fi sani da 'Bobo', a ofishinsu da ke kan titin zuwa Zaria a garin Jos, babban birnin jihar Filato.

Da ya ke tabatarwa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) faruwar lamarin, kakakin rundunar OPSH, Ibrahim Shittu, ya ce basu ji dadin abinda ya faru ba.

A cewar Shittu, mai mukamin manjo a rundunar soji, jami'an rundunar OPSH sun samu kiran kar ta kwana a kan al'amuran wasu batagari, har ma suka kama matasa bakwai da ake zagi suna daga cikinsu.

Ya bayyana cewa daga baya sun sallami Bala da wasu sauran matasa hudu bayan sun gano cewa basu da laifi, amma a hanyarsu ta fita daga ofishin, sai wani soja ya yi kuskuren tunanin cewa guduwa zasu, lamarin da yasa ya bude musu wuta.

Bisa kuskure jami'anmu suka kashe Bala - Rundunar Sojin Najeriya

Bala Bobo
Source: UGC

"Da misalin karfe 10:00 na yamacin jiya (Talata), mun samu labarin cewa wasu 'yan kungiyar asiri da 'yan fashi da makami suna ofireshon a yankin Hwolshe.

"Rahoton da muka samu ya nuna cewa batagari suna amfani da dokar kulle wajen tafka aiyukan ta'addanci.

DUBA WANNAN: Ba zan taba saduda ba, toshon faifai ake yadawa - Shekau ya fitar da sabon sako

"Nan da nan jami'anmu suka dira yankin tare da kama wasu matasa bakwai da ake zargin da hannunsu a aikata laifin, kuma nan take aka taho da su ofis domin gudanar da bincike.

"Mun sallami biyar daga cikin matasan bayan bincikenmu ya gano cewa basu da laifi, kuma nan take mu ka umarcesu su bar ofishin.

"Amma, abin takaci, yayin da suke kokarin fita daga ofishin, sai wani jami'inmu ya ti tsammanin guduwa su ke kokarin yi, lamarin da ya sa ya bude musu wuta har ta kai ga asarar ran Rinji Bala," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel